Teya Salat

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah 00 SHARRIN HARSHE

GABATARWA
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin Talikai tsira da Aminci su tabbata ga mafificin Annabawa da manzanni Annabinmu Muhammadu (Saw) tare da mutanen Gidansa da sahabbansa gaba daya Bayan Haka Hakika Harshe yana cikin Gabbai masu Muhimmanci a Jikin Dan Adam kuma shine mafi zama hatsari ga mutum domin shine Gabar da mutum yake magana da ita kuma yake bayyana kaifin hankalinsa da shi sannan da shine yake bayyana abin da ke cikinsa na alheri ko sharri kamar yadda wani mai waqe yace ka kiyaye harshenka domin harshe yana da saurin kashe mutum harshe shine dan aiken zuciya shine yake nuni ga hankalin mutum Harshe wata hanya ce da mutum yake bi kodai ta kai shi Aljanna ko kuma ta kai shi wuta watau shine Qashin bayan samun rabauta ko kuma tozarta da shine mutum yake Ambaton Ubangijinsa yake gode masa yake masa yabo da shine yake karanta Alkur’ani yake salati ga Annabi (Saw) da shine yake umarni da Kyakkyawan Aiki yake hani ga mummunan Aiki da shine yake fadar gaskiya yake kuma umarni da ita da kuma wannan harshe ne yake yin karya yake cin naman mutane yake Gulma yake bada shaidar karya da shine yake zagi yake la’antar mutane yake batsa da mummunan zance da shine kuma yake umarni da yin fasikanci yake hana yin Adalci saboda Girman hatsarin wannan gabar da yawaita1 Illolinta tsakanin mutane muke son mu tunatar da kawunanmu da ‘yan uwanmu dan gane da wadancan Illoli tare da nuni ga cutarwasa akan mutum a addininsa da duniyarsa muna masu fatan hakan zai sanya a guji wadannan illoli kuma a gyara abubuwan da aka yi a baya kuma ya zama hanyar tuba zuwa ga Allah kafin mutuwa
Allah ya datar damu ya kuma Ishemu madalla da madogara Allah
muhadu a fitowa ta (1) Insha Allahu ta’ala
2018-01-02 14:32 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 29 user
This Week : 110 user
This Month : 352 user
Total all : 270618 visitors
LAST PAGES