Ring ring

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah A SIYASANCE YAN SHI’A DA SUNNAH SUKE YAKI BA DA ARNA BA!!!!(1)

==========================
TANBIHI GA MASU AMINTA DA JAGORANCI KO SHUGABANCIN YAN SHI’A A SIYASANCE.
Kafin mu shiga cikin rubutun namu zai kyau mu lura da wadannan abubuwa da zamu ambato na halayyar Shi’a ada da yanzu,dukka wadannan abubuwa kuwa sun samu ne saboda samun dama da Yan Shi’a sukayi a siyasance da sunan dai-daito ko babu ruwarmu da Addini sai siyasa.
(1) MATSALAR QARAMIDA
Yakar musulunci da Shi’a suka yi na farko kuma mai muni,shine na Karamida a garin Makka,a cikin masallacin harami.A cikin shekara ta dari uku da kwana goma da sha bakwai Yan Shi’a suka shigo sukai ta kashe mahajjata suna kwace masu kudi.Har Shugaban su mai suna Abu Dahir Alqurmidiy ya zauna a kofar Ka’aba yana cewa : “Nine Allah,kuma daga Allah nake,Yana halitta,ni kuma ina karar dasu” yasa a zuba gawarwakin Musulmai cikin rijiyar Zam-Zam,yasa aka rusa kariya rijiyar Zam-zam,Sannan ya bada umurni a tumbuke kofar Ka’aba,kuma yasa aka tube rigar Ka’aba aka yayyaga ya rabawa mutanensa.
Yasa aka tumbuke Dutsen Hajarul Aswad,ganin haka ne aka samu wani Mutum daga cikin Musulmai ya taso domin nuna bai yarda da haka ba,nan take jagoran Yan Shi’an yasa hannu ya buge shi,Anan ne yaji wata muguwar magana ta izgilanci,Inda Shi Shugaban Yan Shi’an yace: “Aina Dairal ababil! A karshe dai, har tsawon shekara ishirin da biyu dutsen Hajarul Aswad yana wurinsu a garin Baharain.
Ibnu Kasir yace,Wani Mutum yace ina cikin Masallacin harami a lokacin da Shi’a Karamida suka dauke dutsen Hajarul Aswad. Har wani mutum cikin su ya shigo ya daure dokinsa a cikin Masallaci,har dokin yayi fitsari a cikin Masallacin,shi kuma yana fadan cewa kunce: “Duk wanda ya shiga cikin sa ya amintu.
(Duba: “Albidayah Wan nihaya 2/156-107”)
MATSALAR ALYU IBNU YAQDIN
Malamin Shi’a wanda ake kiranshi da suna Aljaza’iriy Yace: “Tabbas Aliyu Ibnu Yaqdin,a matsayin shi na wazirin Arrashid,Ya tattara Ahlul Sunnah su dari biyar cikin kurkuku ya ruso rufin dake samansu,rufin kuma ya fado masu,dukkansu ba wanda ya tsira,suka mutu gaba daya su dari biyar.Daga nan ne ya aika wajen Imaminsu dangane da wannan aiki da yayi,menene hukuncin hakan? sai Imamin ya bashi amsa da cewa: “Wannan aiki da kayi yayi daidai,amma mai yasa baka nemi izinin kashe su da farko ba? Kaffarar ka akan wannan aiki shine ka yanka bunsuru guda daya,duk da cewa bunsuru yafi su.Daga wannan ne ya sa kaffara ga Dan Shi’a Idan ya kashe Ahlul Sunnah,shine ya zubar da jini bunsuru guda daya,kuma har ma wai bunsuru din yafi Ahlul Sunnah.
A karshe Aljaza’iri hamshakin Dan Shi’a yayi ta’aliki akan wannan magana,inda yace: “Ka duba wannan sakamako da bai yi dai-dai da diyyar karamin dan uwansa ba karen farauta (Ahlul Sunnah).
(Duba: “Al-Anwarul Nu’umaniyya 2/308,na Ni’imatullah Aljaza’iriy”)
MATSALAR IBNU ALKAMI DA TATAR A BAGDAD.
Cikin dukkan barnar da Shi’a sukai wa Musulunci babu barnar da takai ta waziri Ibnu Alkami yayi,shi wannan waziri Dan Shi’a ne,Babban Malamin tarihin Musulunci,Ibnu Kathir Yace: “A Shekara ta dari shida da hamsin da shida (656) bayan hijira,shi wannan munafikin wazirin Ibnu Alkami ya hada kai da wasu arna ana cewa dasu Tatar,sunan Shugabansu Holakoo Khan,suka afkawa Bagdad.
Wannan abu ya faru ne a lokacin Khalifancin Mu’utassim Billah,wannan barna itace sanadiyyan kawo karshen mulkin Banul Abbas.
Shi wannan Dan Shi’a,Allah ya kara tsine masa albarka ya yaudari Sarkin Musulmi Mu’utassim Billah kuma ya hada kai da Holakoo Khan domin wai sun yi masa alkawarin in suka kashe Khalifa zasu bashi Khalifanci.
A takaice dai wadannan Tatar din sun shigo da mayaka cikin Bagdad har dubu dari biyu (2000,00)ban da sauran Yan Shi’a da suka tarar a garin.Sai da suka kwana Arba’in (40) suna yanka Musulmi Ahlul Sunnah.Bayan sun kashe Khalifa Mu’utassim,sai da takai Mutum saboda wuya sai ya fada cikin rijiya ko ya tona rami a makabarta ya shiga ya buya.Wadansu in suka rasa yadda zasu gudu saboda wuya sai su kai kansu,su kwanta ana yanka su daya bayan daya,Innalillahi Wa Inna’ilaihi raji’un.Ibnu Kasir Ya ce: “Malamai sunyi sabani wajen Iyakance adadin Musulmin da aka kashe,wasu sunce dubu dari da dubu dari takwas,wasu sunce dubu dari takwas ne,wasu sunce dubu dari biyu sau biyu,Kai! Wasu sun ce ma Miliyoyi ne.
Allahu Akbar,Ya mai karatu,warin gawarwaki na Musulmai sai da ya gurbata yanayin iska ya dumama yanayin sararin samaniya na Bagdad.Wanda ya zama sababin annoba a kasar Sham(Syria) a yau,Idan iska ta kado warin daga Bagdad ta kai Sham,mutane suka shaka,kawai sai su mutu,Subhanallah,labari dai babu dadin ji,don haka wasu Malaman tarihi kamar Ibnu Asir yake cewa larura ce ta sanya shi yake rubuta wannan tarihin.
(Duba”Abidayah Wan Nihaya 13/185-189,na Ibnu Kasir”)
Zamu cigaba a rubutu na gaba,Insha Allahu.
Najeeb Elkabir Kwarbai.
2017-12-17 21:02 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 239 user
This Week : 533 user
This Month : 775 user
Total all : 271041 visitorsUnited States
LAST PAGES