XtGem Forum catalog

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah 001 AURE KO MAKARANTA?
Wallafar: *Shaikh Muhammad Abdullah Assalafiy*
Rubutu na 1
GARGAƊI
Haƙƙin mallaka © Muhammad Abdullaah Assalafiy
Ba a yarda wani ko waɗansu su sarrafa wannan littafin ta kowace irin hanya ba sai tare da samun rubutaccen izini da kuma takardar amincewa daga mawallafin
*HADUWAR DATTIJO DA MATASHI*
Dattijo: Habubakar! Na kuwa gaya maka cewa: Zan yi wa ’yata aure?
Matashi: Yarinyar wajenka? ’Yar shekara sha-uku..? Mai ƙoƙarin nan a makaranta?!
Dattijo: Ita fa!
Matashi: A’a, Baba! Ban da garaje! A bar ta ta kammala karatunta tukuna!
Dattijo: Haka kake gani ko?
Matashi: E! Domin tana da ƙoƙari a makaranta. Idan ta samu ilimi, za ta zama babbar mutum. In kuwa aka yi mata aure kuma ta samu juna-biyu, wannan zai cuci iliminta da lafiyarta da ma rayuwarta gaba ɗaya!
Dattijo: Amma shi mai nemanta da auren ne, ya ƙagara a yi auren!
Matashi: A’a! Ya jira ta…! In dai yana son ta da gaske ne, to ya jira ta!
*MAFARIN MAGANAR*
Duk wanda rediyonsa yake kama tashar Kaduna a ’yan kwanakin nan, ba zai rasa jin waɗannan kalmomin ba. Asalinsu kuma daga waɗansu maƙiyanmu ne kuma maƙiya addininmu da kyawawan ɗabi’unmu da al’adunmu. Waɗanda kuma suke ƙoƙari, ba-dare ba-rana wurin lalata mana duk wata kyakkyawar tabiyyar da muke da ita.
Su ne dai masu ƙoƙarin halatta mana abubuwan da Allaah ya haramta, kuma su haramta mana abubuwan da Allaah ya halatta.
Saboda tsananin iya makircin waɗannan maƙiyan ga shi a yau har sun yaudari masu yawa daga cikin jama’armu, ta yadda har waɗansu sun fita batun yi wa ’ya’yansu mata aure, ko da kuwa su ’ya’yan sun buƙatu ga hakan kuma sun samu mazan da suke son su! Kai! Akwai ma waɗanda aka ce su suka ɗaure wa ’ya’yan nasu gindi har suka kashe auren nasu, suka rabu da mazansu na aure domin kawai su dawo su shiga makarantar boko!
Allaah ya kyauta.
To, domin rushe makircin irin waɗannan mutanen, da bayyana gaskiya ga al’ummarmu, musamman waɗanda suke sha’awar rungumar kowane irin sabon shiri da bature ya kawo ba tare da lura, ko gwada shi da dokokin Ubangijinsu da kyawawan al’adun iyayensu da kakanninsu ba, kuma domin sauke nauyin da Allaah Maɗaukakin Sarki ya ɗora wa duk wanda ya sani, na yin nasiha da bayanin gaskiya da adalci ga jama’a, shi ya sa na ga dacewar in gabatar da waɗannan tambayoyi guda ɗari ga iyayen ’ya’ya mata, musamman waɗanda kalaman can na gidan rediyo suka fara burge su.
Ina fatar, bayar da amsoshinsu a bisa gaskiya kuma tsakani da Allaah zai taimaka wurin nuna hanyar gaskiya a cikin al’amarin in shaa’al Laah.
Allaah ya ba mu dacewa.
Dan uwanku: *Muneer Yusuf Assalafy*
Daga: *MAJLISIN SUNNAH*
2017-12-14 21:24 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 44 user
This Week : 44 user
This Month : 997 user
Total all : 271263 visitors
LAST PAGES