Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah JAGORAN MATAFIYA (fitowa ta 1)

JAGORAN MATAFIYA
Wallafar : Sheik Dr. Abdullahi Sale Pakistan Kano
( Ladabi Na Daya )1
Neman Zabin Allah
Ya zama wajibi ga wanda ya yi nufin yin tafiya ya nemi zabin Allah tsarkakakken Sarki dangane da lokaci ko abin hawa ko neman zabin hanyar da ta dace ya bi, idan hanyoyin suna da yawa kuma ya nemi shawara daga kwararru kan harkar tafiya.
Siffar Yanda Ake Neman Zabin Allah ( Istikharah )
Kamar yanda hadisi ya zo daga Jabir dan Abdullahi Allah Ya kara musu yarda, ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi, ya kasance yana koya mana ( istikhara ) a cikin dukkan al’amura kamar yanda yake koyar da mu karatun sura daga Alkur’ani, yana cewa: ” Idan dayanku ya himmatu da yin wani al’amari ya yi Salla raka’o’i biyu ( na nafila ) sannan ya ce; ya Ubangiji ina neman zabinka daga iliminka, kuma ina neman kaddarawa da ikonka kuma ina rokon ka daga falalarka mai girma, lalle kai ne kake da iko ni ba ni da ikon komai kuma kai ne mafi sani ni bani da sani, kai ne masanin abubuwan da ke fake Ya Ubangiji, idan ka san wannan al’amari alheri a gare ni a addinina da rayuwata da karshen al’amari na, ko a karshen rayuwa ta duniya da lahira, Ka juyar min da shi kuma Ka juyar da ni daga gare shi kuma Ka canza min shi, Ka yardar min shi a zuciyata, ( sai mutum ya ambaci bukatarsa ) Bukaari ne ya ruwaito shi. ( 1109 ).
Muhadu a fitowa ta gaba ……………
DAGA
ABDULLAHI
NAGEGIME
2018-02-12 03:28 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 2 user
This Week : 184 user
This Month : 426 user
Total all : 270692 visitorsUnited States
LAST PAGES

Old school Swatch Watches