Teya Salat

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah 001 JININ DABI’A GA MATA

RUBUTU NA 1
.
FASALI NA FARKO
ACIKIN MA’ANAR JININ HAILA DA HIKIMARSA !!!
.
HAILA A LUGGA: shine kwararar abu da kuma gudanarsa.
.
A SHARI’A: shine jini da yake faruwa ga mace na dabi’a ba tare da wani sababi ba acikin wasu sanannun lokuta. Shine jini na dabi’a ( mai zubowa) ba tare da wani sababi na rashin lafiya ba ko rauni ko zubewar ciki ko haihuwa ba.
.
Saboda cewa shi jinine na dabi’a don haka yana sa6awa gwargodon halin mace da yanayin tasowarta da tsufanta, saboda haka mata suna sassa6awa a cikinsa sassa6awa mabanbanta na zahiri.
.
HIKIMA A CIKINSA: yayin da dan tayi ya kasance acikin mahaifiyarsa bazai yuwu ya ringa yin kalaci da irin abunda mutum na wajen ciki yake yin kalaci dashi ba. Kuma bazai yuwu ga wanda yafi kowa tausayinsa ba ya iya sadar da kalaci gare shi (ta kowace hanya ba) saboda haka sai ALLAH (SWT) ya sanya jijiyoyin jini acikin mace wanda ta hanyar sune dan tayin da yake cikin mahaifiyarsa zai dinga yin kalaci acikin mahaifiyarsa ta hanyar cibiya jinin zai dinga shiga ta jijiyoyin d’an cikin yayi kalaci dashi. Tsarki ya tabbata ga ALLAH mafi kyawun masu halitta.
.
Wannan shine Hikimar wannan HAILA saboda haka idan mace ta dauki ciki sai haila ta yanke mata sai ‘yan kadan ne ke yin Haila idan suna da ciki haka kuma masu shayarwa kadan ne ake samun wacce take yin Haila a cikinsu, musamman a farkon lokacin shayarwa.
.
Anan zan dakata, zan cigaba inshaa ALLAH.
^^^ZAUREN MUSLIM UMMAH^^^
.
LITTAFI: JININ DABI’A GA MATA.
.
WALLAFAR: SHEIKH MUHAMMAD SALIH AL’UTHAYMEEN.
.
FASSARAR: UTHMAN MUSA GABARI
.
MAI GABATARWA: FARIDAH BINTU SALIS
(Bintus~sunnah)
2018-01-03 11:25 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 39 user
This Week : 39 user
This Month : 992 user
Total all : 271258 visitors
LAST PAGES