XtGem Forum catalog

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah 001 RADDIN DR ALIYU MUH’D SANI GA WANI ‘DAN ‘KUNGIYAR SALAFIYYUN

..
SURURIYYA
..
Amfani da sunan “Sururiyya” daidai yake da amfani da sunan “Madakhila”, wato suna ne da ake kiran wadanda suka tasirantu da Shaikh Muhammad Surur Zainul Abideen, kuma kamar haka ake amfani da sunan “Madakhila” ana kiran wadanda suka tasirantu da Shaikh Rabee’i Al-Madkhaliy. Don haka in an kira wadancan da Kungiya ko abin zargi to haka wadannan ma Kungiya ne kuma abin zargi. Amma ni ba na son amfani da irin wadannan sunayen, saboda abin yake ciki na jifan mutane da laquba, alhali Allah ya hana mu haka. Sai dai kuma in ya shiga babin Ta’arifi ne.
..
Duk da cewa; wannan mai rubutu bai bayyana a fili cewa; raddi yake yi ga wani rubutu da Aliyu Muh’d Sani ya yi jiya a Facebook ba, amma sai dai in ka lura da abin da ya kunsa da kuma lokacin zuwansa, sai ka ga hakika raddin ne, amma sai aka guji kama suna. To in raddi ne ga rubutun Aliyu Muh’d Sani, menene alakar rubutun Aliyu da Sururiyyah?
..
Mai rubutun ya ambaci littafin Shaikh AbdulMalik Ramadhaniy, ya ce; yana cikin manyan littatafan da suka tona asirin Sururiyya, kuma Shaikh Albaniy da Shaikh Abbad ne suka duba littafin, sai ya yi tambaya kamar haka:”Shin suma yan kungiyar salafiyyuun ne ko gulatut tabdeei”?.A’a, ai Shaikh Ibnu Uthaimeen da ya kira masu Kungiyanci da sunan Salafiyya da kuma Guluwwi, da sunan Kungiyar Salafiyyun ba don suna tona asirin Sururiyyun ba ne, a’a, kawai don ya tabbatar da samuwar Kungiyancin ne a cikinsu,tare da kulla wala’i da bara’i a kan wasu malamai ko mas’aloli na Ijtihadi, shi ya sa ya kira su da hakan. Kuma hatta shi Shaikh AbdulMalik Ramadhaniy a yau yana cikin masu sukan ‘Yan Kungiyar Salafiyyun da kiransu ko siffanta su da sunan Gulatut Tabdee’i/ Tajrihi. Don haka ba don tona asirin Sururiyyun ne ya sa ake kiran Gulatut Tabdee’i da sunan ‘Yan Kungiyar Salafiyyun ba. Mayar da dalilin kiransu da sunan zuwa ga tona asirin Sururiyyun, kawai dabara ce ta dauke hankalin mutane, da kokarin boye hakika.
..
Mai rubutun ya ce:”Shek Albany yace musu Kawarijawan zamani”.Mai rubutun yana nufin Shaikh Albaniy ya bidi’antar da Sururiyyun, alhali in ka koma asalin maganar Shaikh Albaniy sai ka ga lamarin ya banbanta da abin da marubucin ya yi da’awa.Ga asalin maganar Shaikh kamar haka lokacin da aka ce masa:(::.:”:: :–--- – :!!(! !: ”…Na farko dai, Shaikh Safar Hawaliy shi ne mai wancan littafi da aka ambata a sama mai suna:Wanda a cikinsa ne ya jingina Irja’i ga Shaikh Albaniy. Na biyu: in ka lura da maganar Shaikh sosai, za ka ga bai yanke musu hukuncin Khawarijanci ba. Wannan ya sa a karshe ya ce:: Saboda haka, kafa hujja da wannar magana ta Shaikh Albaniy a matsayin ya kira su da ‘Yan Bidi’a, Khawarijawa yana bukatar sake nazari.Sa’annan kuma rubutun da Aliyu Muh’d Sani ya yi ba ya yi ne don kare Shaikh Safar ko Salmanul Auda ba, balle a yi masa ilzami da wannar magana, ya yi ne don nuna lokacin da Kungiyar Salafiyyun suka fara bayyana, har Shaikh Ibnu Uthaimeen ya ambaci sunan, sa’annan Shaikh Abbad ya rubuta littafinsa:Don haka ko da ba Sururiyyun Shaikh Abbad yakenufi ba, bidi’antar da Ahlus Suannan da Shaikh Abbad yake nufi yana daga cikin farko – farkon bullar fitinar Guluwwi a Bidi’antarwa da bullar Salafiyya ta kungiya kamar Kungiyar Ikhwan da Tableeg.
..
Mai rubutun ya ce:”Don haka kai mai kare malamanka kasan abinda zaka karesu dashi. Abinda ya kamata ka nemi hujjar barrantar dasu daga sururiyya da manhajinsu na bidi’a.” Toh, In da Aliyu Muh’d Sani yake to Safar da Salman ba Malaman Aliyu Muh’d Sani ba ne, kuma bai taba kare su. Don haka babu munasaba a tsakani. In kuma su Shaikh Ja’afar da Albaniy Zaria yake nufi, wadanda kwanakin baya muka yi rubutu don yin raddi ga Lekca ‘yar Ghana da a cikinta aka kira sunayen Malamai ‘Yan Nigeria aka bidi’antar da su ta hanyar kiransu da Sururiyyun, to a nan ma sai in ce: ba kare su aka yi ba, ba su uzuri aka yi. Don da yawa daga cikin mutaneba sa banbanta tsakanin kariya da ba da uzuri. Kariya shi ne ka nuna abin da suka yi na kuskure daidai ne ba kuskure ba ne. Amma ba da uzuri kuma shi ne ka yarda sun yi kuskure amma kuma suna da uzurin da Mai Lakca ‘yar Ghana da ire – irensa ba su kai matsayin su Bidi’antar da su ba. Su ‘Yan Kungiyar Salafiyyun suna daukar su Malam Ja’afar a matsayin Sururiyya ‘Yan Bidi’a ne saboda Al-Muntada ta Muh’d Surur, shi ya sa shi mai wannan rubutu ya fadi wannar magana tasa, alhali bayan sun yi Lakcar Ghanan, Malaminmu Dr. Birnin Kudu ya yi wa Duniya bayanin cewa; shiga cikin Almuntada kawai ba shi zai sa wadannan malaman su zama ‘Yan Bidi’a ba. Kai, bayan waccar lekcar Ghanan, akwai wata magana da Malam ya fada mini kamar haka, inda ya ce:”Ban ga dalilin da zai sa in dubi masu yakar bidi’a irin su Dr Sani ba in ce musu yan bid’a”. Yana nufin shi ba ya Bidi’antar da su Dr. Sani R/ Lemo da ire – irensa masu yakar Bidi’a, wadanda suke da alaka da Al-Muntada.
..
Mu tara a cigaban raddin na gaba.
2017-12-31 00:09 (edited 2017-12-31 00:23 by ibnhujjah ) · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 143 user
This Week : 437 user
This Month : 679 user
Total all : 270945 visitorsUnited States
LAST PAGES