Snack's 1967

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah 001 SHARRIN HARSHE

Allah maɗaukakin sarki yace Babu wata magana da zai furta face akwai mai tsaro a tare dashi Halartacce (Suratul Qaf 18) Shahararren malamin tafsirin nan wato malam Ibnu Kasir (RH) ya fada dangane da wannan aya Babu wata Kalma Da Dan Adam zai fada face sai an sa mata wanda zai rubuta ta ya Ajjiye masa ita kamar yadda Allah maɗaukakin sarki yace
Lallai akwai masu kiyaye duk abin da kuka yi masu daraja marubuta suna sanin duk abinda kuke aikatawa ( Infidar 10-12) lallai ya kamata ga duk mai Hankali ya kiyaye harshensa ta hanyar tsarkake shi kada yayi wata magana sai idan akwai amfani a ciki wannan kuwa ba abu ne mai sauki ba yana bukatar jajircewa da tilastawa kai har sai ya saba fadar Alkairin kawai kuma hakan ta zama dabi’arsa ya kuma guji fadar sharri tare da kin hakan a zuciyarsa Muhammad dan wasi’u ya fadawa malik dan Dinar cewa ya kai baban Yahaya ka sani cewa kiyaye harshe yafi wahala a kan kiyaye dinare (kudi) Abdullahi dan Abbas Allah ya kara masa yarda ya gayawa harshensa cewa kai harshe ka fadi alheri sai ka rabauta ko kayi shuru kada ka fadi sharri sai ka kubuta Wasu masu Hikima sunce harshe shi take bayyana girmansa da darajarsa itace kuma take nuna kaifin hankalinsa saboda haka ka karanta maganarka akan abu mai kyau kawai kuma kada ka tsawaita
Wani mai waqen Larabci yace ka Auna magana kafin kayi domin magana itace take fito da aibin mai aibi
Wallafar malama Hafsa sani Buhari
….
Muhadu a fitowa ta (2) Insha Allahu ta,ala
2018-01-02 14:05 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 19 user
This Week : 100 user
This Month : 342 user
Total all : 270608 visitors
LAST PAGES