Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah 002 AURE KO MAKARANTA ?
Wallafar: *Shaikh Muhammad Abdullah Assalafiy*
Rubutu na 2
GARE KU IYAYEN ’YAN MATA
1. Yaushe ne kammala makaranta ya zama ɗaya daga cikin rukunnai ko sharuɗɗan aure?
2. Kakanni ko iyayen da suka haife ku suna da karatun aji nawa ne aka yi musu aure?
3. Ku kuma kuna cikin aji nawa ne aka fitar da ku aka yi muku naku auren?
4. Yaya yawan shekarunku da girman jikinku a lokacin?
5. Me za ku iya faɗa game da muguwar sha’awar jima’i kafin yin aure?
6. A tsakanin sabuwa da tsohuwar balaga wacce ce ta fi samun ƙarfin sha’awa?
7. Akwai yaɗuwar littaffan labarai da hotunan batsa a tsakanin matasa a lokacinku?
8. Shin ko waɗannan labarun da hotunan suna taimakawa wurin motsar da sha’awa?
9. Akwai cuɗanya sosai a tsakanin maza da mata a zamanin da kuke matasa?
10. Shin irin wannan caɗanyar tana taimakawa wurin motsar da sha’awa ko ba ta yi?
11. Bayan gama tarewar aurenku haƙurin watanni nawa kuka iya yi kafin fara saduwa?
12. Duk da tsufanku a yanzu haƙurin kwana nawa kuke iya yi?
13. Shin ko kun san wani magani na muguwar sha’awar jima’i kuwa?
14. Kun ba ’yarku wannan maganin kuma ta yarda tana amfani da shi yadda ya dace?
15. Yanzu saurare ko karatun labarun batsa ba su motsar da sha’awarta?
16. Kun tabbata kallon hotunan batsa a cikin mujallu da akwatunan talabijin ba sa motsa mata sha’awa?
17. Kun sakankance cewa hira da samari a ƙofar gida bayan magariba ba ta motsa mata sha’awa?
18. Kun san irin mutanen da za ta yi hulɗa da su a cikin makarantar kuwa?
19. Kun gamsu cewa hulɗar ta da ƙawaye da samari a makarantar ba za su ɓata mata tarbiyya ba?
20. Kuna tsammanin tsagwaron karatun bokon ne kaɗai za ta koyo a makarantar?
21. Kuna da cikakken sanin duk abubuwan da sukan faru a cikin makarantun nan kuwa?
Dan uwanku: *Muneer Yusuf Assalafy*
Daga: *majlisin sunnah*
2017-12-14 21:27 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 32 user
This Week : 32 user
This Month : 985 user
Total all : 271251 visitors
LAST PAGES

80s toys - Atari. I still have