Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah JAGORAN MATAFIYA

Fitowa ta biyu
Wallafar : Sheik Dr. Abdullahi Sale Pakistan Kano
( Ladabi Na Biyu ) 2
Matafiyi Ya Nemi Yardar Allah
Ya zama wajibi ga mai aikin Hajji ko Umara ya yi nufin neman yardar Allah ga aikin Hajjinsa ko Umararsa kuma ya yi taka-tsantsan, kada ya nufi al’faharin duniya ko fariya ko riya ko don ace masa Alhaji, domin yin haka yana sabbaba lalacewar aiki da rashin karbuwarsa.Allah madaukakin sarki ya ce: “kace lallai sallata da yankata da rayuwata da mutuwata ga Allah Ubangijin halittu Suke Shi kadai babu abokin tarayya a gare shi da haka aka umarce ni kuma nine farkon mai mika wuya gare shi.” Suratul An’am: 162-163
Kuma Allah madaukakin Sarki ya ce: “Ka ce ni mutum ne tamkarku, sai dai ana yimin wahayi a gareni, cewa Ubangijinku abin bautarku, Ubangiji ne guda daya, duk wanda ya kasance yana kaunar haduwa da Ubangijinsa, ya yi aiki na kwarai, kada yayi shirka da a bautawa Ubangijinsa tare da wani.” Al’kaffi 110.
Kuma Allah madaukakin Sarki ya ce: “Wanda ya kasance yana nufin magaggauciya ( Duniya ) zamu gaggauta ba da abin da mukaga dama ga wanda mukaga dama, sannan mu sanya wutar jahannama makoma gare shi, ya shige ta yana abin zargi kuma yana kaskantacce .” Isa’i: 18.
Kuma yazo a cikin Hadisin kudusi ; Allah ya ce: “Ni ne mafi wadatuwa daga shirkar masu shirka, wanda duk ya aikata wani aiki yayi shirka a cikinsa, to, zan bar shi da shirkarsa.” Musulimu ne ya ruwaito shi a cikin littafin Zuhudu, Babin wanda ya yi shirka da Allah a ciki aikinsa, lamba : 2985
Muhadu a fitowa ta gaba ……………
DAGA ABDULLAHI NAGEGIME
2018-02-19 01:36 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 34 user
This Week : 216 user
This Month : 458 user
Total all : 270724 visitors
LAST PAGES

XtGem Forum catalog