Duck hunt

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah 002 JININ DABI’A GA MATA

RUBUTU NA 2.
.
FASALI NA BIYU: CIKIN ZAMANIN HAILA DA GWARGODONSA.
.
Zance acikin wannan fasalin yana da matsayi guda 2.
.
MATSAYI NA FARKO: A cikin shekarun da haila take zuwa acikin su.
.
MATSAYI NA BIYU: A cikin lokacin Haila.
.
Amma MATSAYI NA FARKO shekarun da haila tafi rinjaye acikinsu shine: tsakanin shekara 12 Zuwa shekara 50, amma ana samu sau da yawa mace tana yin haila a kafin haka ko bayan haka gwargodon halinta da tasowarta da kuma tsufanta. Lallai malamai sunyi sa6ani akan shin shekarun da haila take zuwa aciki suna da iyaka da aka ayyana ta yadda mace ba zatayi haila gabanninsu ba ko bayansu. Kuma shin jinin da yake zuwa ga mace a gabanninsu ko bayansu jinin haila ne ko na cuta? Malamai sunyi sa6ani acikin wannan.
.
Darimiy yace: Bayan ya kawo sa6anin: dukkan wadannan kuskure ne awajena domai a baki dayan wannan yana komawa ne izuwa samuwar jinin, duk jinin da ya samu a kowani hali da shekaru, ya wajaba a sanya shi a matsayin haila. Wallahu a’alamu. (Al-majmu’u sharhil Muhazzab 1/336)
.
Wannan abunda Darimiy ya fada shine daidai, kuma shine za6in Sheikhul Islam Ibn Taimiyyah. Wato duk sanda mace taga haila to ita mai haila ce koda bata cika shekara 9 ba ko kuma ta wuce shekara 50. Wannan kuwa saboda ALLAH da Manzonsa (SAW) sun rataya hukuncin haila ne bisa suwarsa. Kuma ALLAH da Manzonsa (SAW) basu iyakance wasu ayyanannun shekaru ba game da wannan ya wajaba komawa zuwa sumuwar jinin wanda aka rataya hukunce hukunce a kansa. Iyakance shi da ayyanannun shekaru yana buqatar dalili daga Qur’an ko sunnah. Gashi kuwa babu dalili akan haka.
.
Anan zan dakata inshaa ALLAH a rubutu na gaba zamu tashi daga kan MATSAYI NA BIYU.
^ZAUREN MUSLIM UMMAH^^^
.
LITTAFI: JININ DABI’A GA MATA.
.
WALLAFAR: SHEIKH MUHAMMAD SALIH AL’UTHAYMEEN.
.
FASSARAR: UTHMAN MUSA GABARI.
.
MAI GABATARWA: FARIDAH BINTU SALIS
(Bintus~sunnah)
2018-01-03 11:29 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 41 user
This Week : 41 user
This Month : 994 user
Total all : 271260 visitors
LAST PAGES