Insane

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
Muhammad Ishaq 002 LADUBBAN TAREWA

Rubutu na 2
*Yadda Ake Yin Bikin Aure*
Bikin aure wanda ya ƙunshi yayata shi da bayyana shi abin so ne, in ji malamai saboda dalilai masu yawa kamar haka:
Maganar Annabi (Sallal Laahu ’Alaihi wa Aalihi wa Sallam) cewa: Bambancin da ke tsakanin halal da haram shi ne, buga dundufa da jin muryar (waƙa a wurin aure). ²
Kuma a lokacin da su A’ishah r.a suka kai wata amarya gidan mijinta sai Annabi (Sallal Laahu ’Alaihi wa Aalihi wa Sallam) ya ce: A’ishah! Ba ku da wadda za ta yi ɗan waƙa ne, domin su Lansarawa mutane ne da suke sha’awar wasa. ³
Wannan ya nuna abubuwa kamar haka:
° Ya halatta waɗansu mata masu mutunci su raka amarya zuwa gidan mijinta a ranar tarewarta. ⁴
° Kuma in aka samu wata mai rera waƙar aure irin na al’ada a cikinsu duk ya yi daidai.
° Daidai ne kuma matan da suka kai amaryar su zauna a gidan amaryar kuma su saurari irin wannan waƙar.
Sannan kuma ga Aamir Bn Sa’ad ya shiga wurin Ƙarazah Bn Ka’ab da Abu Mas’uud Al-Ansaariy a lokacin wani angwanci, sai kuma ya ga waɗansu kuyangi suna waƙa. Don haka sai ya ce: Haba! Ga ku fa sahabban Manzon Allaah (Sallal Laahu ’Alaihi wa Aalihi wa Sallam) kuma mutanen Badar ne, amma kuka bari ana yin wannan a gabanku?! Sai suka ce: Ka zauna ka ji tare da mu in kana buƙata, domin an yi mana sassauci ga sauraron waƙe irin wannan a lokacin bikin angwanci. 5
• Kuma a lokacin da aka yi wa Ar-Rubayyi’u bint Mu’awwiz aure kuma Manzon Allaah (Sallal Laahu ’Alaihi wa Aallihi wa Sallam) ya tafi domin gaishe ta, sai waɗansu kuyangi suka fara buga dundufa suna waƙen yabon iyayenta da suka yi shahada a yaƙin Badar. Ana cikin haka ne sai wata daga cikinsu ta ce: Kuma a cikinmu akwai Annabi yana sanin gobe!
A nan ne sai Manzon Allaah (Sallal Laahu ’Alaihi wa Aalihi wa Sallam) ya ce: Rabu da wannan, ke dai ki cigaba da faɗin abin da kike faɗi a da!6
Wannan ya nuna har manya ma sun tafi gidan amarya kuma sun zauna sun taya ta murna, har kuma ma sun saurari kiɗa da waƙar aure a lokacin.
Amma yaya ake yin wannan kiɗan da waƙar?
Malamai sun ce ana yin wannan abin ne kamar yadda Hadisan suka nuna:
• Ayi amfani da gangar da ake kira dundufa kawai ban da wadda ba ita ba.
• Kuma ayi waƙar da irin kalmomin da suka halatta a shari’a, ba da kalmomin da aka hana a shari’ar ba.
• Mata ne kaɗai suke yin kiɗa da waƙar amma ba maza, ko maza da mata a cakuɗe ba!
Amma bukukuwa da wasannin auren da ake yi a yau sun saɓa wa waɗannan ƙa’idojin, saboda dalilai kamar haka:
• Ana amfani ne da kayan kiɗa irin na zamani kamar goge da molo da kalangu da algaita da makamantansu.
• A cikin waƙoƙin ana amfani da mugayen kalmomin batsa masu siffata mata da giya da sauran ayyukan fasiƙanci.
• Kalmomin suna zuga matasa ga aikata ayyukan alfasha na zina da shaye-shaye da sauran ayyukan saɓon Allaah.
• Uwa uba kuma shi ne inda ake samun cakuɗa a tsakanin maza da mata a wurin, wanda yake haifar da aukuwar munanan ayyukan assha na zubar da mutunci da sauransu.7
Shi ya sa tun tuni malamai suka yi kakkausar suka a kan irin wannan bikin:
• Ibn Rajab ya ce: Dundufarsu kamar irin manyan gangunan nan ne, kuma waƙoƙinsu irin waƙoƙin zamanin jahiliyya ne, irin waɗanda suka saba yi a lokutan yaƙi da makamantan haka.
To, duk wanda ya yi ƙoƙarin kamanta wannan da sauraron irin waƙoƙin batsa da ake haɗa su da kayan kiɗa ko busa ko garaya, to babu shakka ya yi babban kuskure. Domin ya yi ƙiyasi ne tare da samuwar bambanci a tsakanin tushe da reshe!
• Al-Izzu Bn Abdis Salaam ya ce: Amma busa da sauran kayan wasa masu igiya kamar molo da garaya da goge, to mashahuriyar magana dai a wurin malaman mazhabobin nan guda huɗu ita ce: Amfani da su da kuma sauraronsu haram ne.8
Babban abin lura dai a nan shi ne:
Kayan kiɗan da aka yarda da amfani da su a wurin bikin aure shi ne dundufa kaɗai, ban da sauran waɗanda suka shiga ƙarƙashin abin da aka haramta.
Hadisi ya tabbata daga Manzon Allaah (Sallal Laahu ’Alaihi wa Aalihi wa Sallam) ya ce: Waɗansu mutane za su kasance a cikin al’ummata waɗanda za su halatta zina da alharini da giya da kayan kiɗa. Kuma waɗansu mutane za su sauka a gefen wani tsauni ana yi musu goge ko garaya a cikinsu, sai mabaraci ya zo musu da buƙatarsa, su kuma sai su ce masa, ka bari sai gobe ka dawo. Sai kuwa a wayi gari Allaah ya hallaka su gaba ɗaya, an ruguza tsaunin kuma an shafe waɗansu, an mayar da su birai da aladu!
Wannan yana daga cikin hadisai da malamai suka inganta a kan haramcin kayan kiɗa.
Hadisin ya nuna haramcin amfani da kayan kiɗa da busa irin na zamani ta hanyoyi da yawa kamar haka:
• Cewa da ya yi: ‘za su halatta’ ya nuna a asali wannan abin ba halal ba ne, wani abu ne daga cikin abubuwan da Allaah ya haramta amma su ne suka mayar da shi halal!
• Haɗa shi da sauran abubuwan da kowa ya san haram ne a wuri ɗaya, watau: zina da giya da sanya alharini, ya nuna hukuncinsu iri ɗaya ne watau haramci.
• Hallaka su da Allaah Ta’aala ya yi wannan ma ya nuna cewa sun aikata haram ne.
• Haka kuma shafe su da aka yi zuwa ga siffofin birai da aladu, wannan ma ya nuna sun
2017-12-23 12:26 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 61 user
This Week : 142 user
This Month : 384 user
Total all : 270650 visitorsUnited States
LAST PAGES