Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah 004 AURE KO MAKARANTA?
Wallafar: *Shaikh Muhammad Abdullah Assalafiy*
Rubutu na 4
Daga: *zauren majlisin sunnah*
*MU YI TUNANI*
39. Menene amfanin ƙoƙarin yarinya a irin wannan makarantar?
40. Menene fa’idar kammala karatun yarinya a irin wannan makarantar?
41. Wace irin babbar mutum ce irin wannan makarantar take yayewa?
42. Menene ya fi rayuwa a cikin irin wannan makarantar cutar da ilimi?
43. Menene ya fi rayuwa a cikin irin wannan makarantar cutar da lafiya?
44. Anya yarinyar kirki za ta iya natsuwa a cikin irin wannan makarantar?
45. Saboda irin wannan makarantar ce za a hana yarinya yi aure?
46. Ba sa’o’in masu shekaru sha-uku ne suka cika irin waɗannan makarantun ba?
47. Yanzu rayuwa a cikin irin wannan makarantar ba aure zai fi rayuwa tare da aure?
*YA JIRA HAR YAUSHE?*
48. Kuna tsammanin shi ne kaɗai tasirin jiran zai shafa?
49. Wanene tsawon jiran zai fi cutarwa: Ita ce ko shi?
50. Kun tabbatar za ta tabbata a kan halinta na-gari a bayan tsawon jiran?
51. Kun amince za ta zama a cikin kyakkyawar surarta na-asali a bayan jiran?
52. Kun amince ba za ta sauya ra’ayinta game da shi ba, a bayan jiran?
53. Kun amince ba za ta karya alƙawarin da kuka yi masa ba, a bayan jiran?
54. Kun tabbata za ta iya haƙurin kame kanta har zuwa ta kammala karatun?
55. Kun amince wani ba zai riga ‘saninta’ kafin lokacin auren ba?
56. Kun riga kun ɗauki waɗansu matakai ne domin tabbatar da haka?
57. Kuna jin za ta iya haƙurin bin mijin bayan kammala karatun?
58. Kuna jin shi saurayin zai iya yin haƙuri na tsawon jiran da kuke so?
59. Kun amince sai in ya jira ta ne, ya nuna yana sonta da gaske?
60. Kuna jin zai riƙe ta da mutunci a bayan tsawon jiran da kuka sa ya yi?
61. Kuna jin zai ga girmanku da mutuncinku bayan tsawon jiran?
Dan uwanku: *Muneer Yusuf Assalafy*
2017-12-14 21:36 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 37 user
This Week : 37 user
This Month : 990 user
Total all : 271256 visitors
LAST PAGES

Insane