XtGem Forum catalog

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah HADARIN FATAWA {4}

SIFFOFIN MAI FATAWA
SANIN HALIN MUTANE DA AL’ADUNSU:-
Wannan wata sifface mai matuqar mahimmanci ga mai fatawa, ya san halin mutanen da yake rayuwa a cikinsu da sassabawar ta’adojinsu, da yanayinsa, domin sune za su riqa yi masa tambayoyi shi kuma ya riqa basu amsa wadda ita ce “fatawa”.
Wani lokaci ana iyama malami mai fatawa tambayoyi biyu iri daya amma amsoshinsu su banbanta domin sanin halayen mutane da su kai wadannan tambayoyi masu kama daya amma da mabanbantan amsoshi.
DOGARO DA KAI A RAYUWA
Tabbas ana buqatar mai bada fatawa ya zamo mai dogaro da kansa don kar ya zama karen farautar wani, ko makamin wani, ko mai gadin wani, domin in hannu ya amsa, baki kuma ya ci, to dole ido ya ji kunya. Shi yasa wata rana aka ga Babban Malami Sufyan al-thauriy a kasuwa yana qirga kudinsa bayan ya gama cin kasuwa, sai aka ce masa: Har da ku malam!? Sai ya ce: ai badan wadannan ba {kudi} da ‘yan duniya sun maida mu {malami} tsimman share majina. Sannan. Babban Malami Ibnul – uthaimen ya kasa malamai zuwa gida uku:-
1- Malaman talakawa, masu son talakawan gari su yarda da dasu, su so su.
2- Malaman hukuma, masu son shuwagabanni su yarda da su, su riqa basu kudi.
3- Malamai na addini na Allah, wadanda suka tsayu da kansu akan gaskiya, Allah kawai suke buqatar ya yarda da su. Allah ka samu a cikinsu.
Allah Ya hada mu a gaba.
Rubutawar:
Basheer Lawal Muhammad Zaria.
2018-01-13 03:24 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 52 user
This Week : 133 user
This Month : 375 user
Total all : 270641 visitorsUnited States
LAST PAGES