Disneyland 1972 Love the old s

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah 004 HUKUNCE – HUKUNCEN JANAZA A SAWQAQE

TAKARDA TA FARKO {1}
WANKA DA ABUBUWAN DA KE DA ALAQA DA SHI
DARASI NA UKU {4}
FALALAR WANKAN GAWA:-
Al-Imam Hakim ya ruwaito hadisi wanda Manzon Allah {S.A.W} yake cewa“Duk wanda ya wanke mamaci, kuma ya rufa masa asiri, Allah zai gafarta masa sau arba’in”. Kuma a wani hadisin Manzon Allah {S.A.W} ya ce “Duk wanda ya wanke mamaci, kuma ya rufa masa asiri, to Allah zai tufatar da shi daga cikin tufafin gidan al-jannah.
SIFFOFIN MAI WANKAN GAWA:-
Daga cikin siffofin mai wankan gawa ya kasance:-
1- Mai ikhlasi {Yi don Allah}.
2- Daga cikin makusantan sa misali: iyaye, kanne ko yayye, ‘ya ‘yansa da sauransu, in ya yuwu.
3- Maza su wanke maza, suma mata su wanke mata {sai dai miji zai iya wanke matarsa haka ma mace zata iya wanke mijinta}.
4- Mai rufa asiri {wato kada ya yada abin da ya gani mara kyau daga gawa}.
Allah shine mafi sani.
Rubutawar:
Yusuf Lawal Yusuf
(Abu Ja’@far)
2018-02-22 13:03 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 18 user
This Week : 200 user
This Month : 442 user
Total all : 270708 visitorsUnited States
LAST PAGES