Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah Wallafar: *Shaikh Muhammad Abdullah Assalafiy*
Rubutu na 6
Daga: *zauren majlisin sunnah*
*MU KOMA GA NASSI*
90. Shin ba Allaah Maɗaukakin Sarki ba ne ya ce:
Kuma ku aurar da marasa aure daga cikinku?
91. Shin lafazin ‘marasa aure’ bai haɗa tsofaffi da sababbin balaga ba?
92. Kuma wannan lafazin na ‘marasa aure’ bai haɗa maza da mata ba?
93. Shin yin gaggawa wurin bin umurnin Allaah (Subhaanahuu wa Ta’aalaa) ba wajibi ba ne a kan dukkan musulmi?
94. Ko akwai wani nassin da ya nuna halaccin dakatar da yin aure domin kawai rashin kammala wani karatu ba ma na-boko ba?
95. Kuma shin ba Annabi (Sallal Laahu Alaihi wa Aalihi wa Sallam) ba ne ya ce:
Idan wanda kuka yarda da addininsa da ɗabi’unsa ya zo muku, to ku aura masa. Idan kuma ba ku yi haka ba, to wata mummunar fitina za ta auku a duniya da ɓarna mai girma’?
96. Shin wannan bai zama babban dalili a kan a gaggauta yi wa duk wanda ya isa aure ba?
97. Kuma shin aukuwan bala’o’i da masifu a yau ba su zama masu tabbatar da gaskiyar wannan Hadisin ba?
98. Jinkirta aure da ƙin gaggauta yinsa bayan haɗuwar rukunnansa bai zama babbar hanyar saɓa wa wannan Hadisin ba?
99. Cewa: ‘Ban da garaje! A bar ta, ta kammala karatunta tukuna’ bai zama saɓa wa wannan Hadisin a fili ƙarara ba?
100. Wannan maganar ba ta zama musifar da ta fi komai cutar da ilimi da lafiya da rayuwar al’umma gaba ɗaya ba?
*A ƘARSHE*
Muna roƙon Allaah Maɗaukakin Sarki ya ƙara tsare mu, ya shiryar da mu baki ɗaya, kuma ya ba mu ƙarfin gwiwar kafewa a kan bin Sunnah har zuwa ƙarshenmu.
Kuma godiya ta tabbata ga Allaah a farko da ƙarshe. Tsira da amincin Allaah su tabbata ga shugaban na-farko da na-ƙarshe, shi da iyalai da sahabbansa da sauran Salihai.
Daga:
Muhammad Abdullaah Assalafiy,
Masjidut Tajwiid,
Zango.
26/Nuwamba/1992.
2017-12-17 10:41 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 47 user
This Week : 47 user
This Month : 1000 user
Total all : 271266 visitorsUnited States
LAST PAGES

Disneyland 1972 Love the old s