XtGem Forum catalog

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah FA’IDAR YIN AURE DA WURI (01)
Aurar da yara Mata da zarar sun balaga, Ko kuma kafin ma su balaga, yana daga cikin halayen Magabata na kwarai. Kuma yana daga cikin hanyoyin da zamu iya bi awannan zamanin domin dakile barna da ayyukan fasikanci wadanda kullum suke Qara ya’duwa acikin al’ummah.
Ba kamar yadda turawan yamma kullum suke kokarin juyar da tunanin al’ummar Musulmai ba, suna cewa wai aurar da ‘ya’ya Mata da wuri yana haifar da chututtuka, yana haifar da lalacewar rayuwa da sauran matsaloli kala-kala, wanda kuma duk Qarya ce zalla. Kuma hujjojin da suke bayarwa akan haka ba karbabbu bane, tunda cututtukan da rashin auren ke haifarwa sunfi girma sunfi muni fiye da duk tunanin mutum.
Yarda da irin wadannan miyagun ra’ayoyin na Turawa yakan sanya wasu daga Jama’ar Musulmai wadanda suke ganin wai kansu ya waye, har suna kallon addininmu da kyawawan al’adunmu kamar wani ci-baya.
Su kansu turawan idan kun duba cikin tarihinsu da tarihin sarakunansu da daulolinsu zaku tarar cewa cike suke da tarihin ‘ya’yan sarakunansu wadanda aka aurar da wuri, har ma suka hayayyafa kuma su turawan suna alfahari dasu.
Hakanan koda acikin Bible dinsu akwai wuraren da suka halatta aurar da yara mata tun suna ‘Yan shekaru biyar-biyar aduniya.
Kuma yanzu haka yaran Turawan Amurka da Ingila da Faransa da sauran Qasashen Turai sukan fara aikata zinace-zinace tun basu fi ‘Yan shekaru sha biyu, sha uku ba. Kafin yarinya ta kai shekaru 20 aduniya ta gama sanin komai tsakaninta da ‘Da Namiji. Kuma su iyayensu basu dauki wannan din abakin komai ba..
Su Turawa a ra’ayinsu Zina ba laifi bane mutukar dai anyita ne bisa soyayya, ko kuma kan ra’ayin masu yinta, ba tilastasu akayi ba. Shi yasa su awajensu aure bashi da wani muhimmancin da za’a kula dashi wajen tsaftace al’ummah.
Amma mu Musulmai awajenmu aure shine jigon rayuwa tunda ta dalikinsa ne ake samun ya’duwar al’ummah managarciya. Kuma aure ibadah ne tunda ta hanyarsa ana samun shiga Aljannah. Aure yana tsaftace al’ummah ya hana barna shiga cikinta. Kuma aure yana gyara halayen masu yinsa, ya hanasu afkawa cikin sa’bon Allah.
Abu ne mai hatsarin gaske a rika Jinkirta ma ‘ya’ya mata da maza yin aure don burin neman abin duniya. Kodai ache wai sai ta gama makaranta ta samu aiki, ko kuma ache ba za’a aurar da ita ga talaka ba. Ana nan ana jiran mai kudi yazo ya aureta. Ba’a la’akari da hali ko yanayin da ita yarinyar zata iya shiga saboda sha’awa ko matsuwarta da yin auren.
Wannan duk tsari ne irin na Yahudu da Nasara wadanda mafiya yawansu sukan Qare Quruciyarsu ne ba tare da yin aure ba.. Kuma basu kawo tunanin mutuwa azukatansu ballantana suyi tanadi dominta.
Ya zama wajibi iyaye kuji tsoron Allah ku rika bin dokokinsa wajen aurar da ‘Ya’yanku da zarar sun samu Manemi na kirki koda kuwa basu kammala karatun bokon ba. Idan shi Mijin yaso sai su koma suci gaba da karatunsu tare da aurensu. Wanda hakan shine daidai idan ma’aurata sunyi tsari mai kyau. Wannan kuma shine yafi alkhairi da kuma kiyaye tarbiyyarsu daga lalacewa.
Ku dubi dai Manzon Allah (saww) duk ‘ya’yansa babu wacce takai shekaru ashirin (20) aduniya kafin yayi aurenta. Ga Sayyiduna Abubakrin Assiddeeq (rta) ya aurar da ‘Yarsa (Nana A’isha) tun tana ‘yar shekaru bkwai (7) aduniya. Kuma ta tare dakin mijinta tana da shekaru tara (9) aduniya.
Sayyiduna Aliyu bn Abi Talib (ra) shima ya aurar da ‘yarsa Ummu Kulsum run bata kai shekaru 10 aduniya ba. Hakanan Sayyiduna Umar bn Al-Khattab (ra).
"HAKIKA KYAKKYAWAN ABIN KOYI YA KASANCE GAREKU CIKIN (RAYUWAR) MANZON ALLAH, GA WANDA YAKE QAUNAR ALLAH DA RANAR LAHIRA ".( SURAH AL-AHZAAB).
WANNAN NASIHA CE DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990
2018-02-09 20:55 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 6 user
This Week : 26 user
This Month : 114 user
Total all : 270380 visitorsUnited States
LAST PAGES