Old school Easter eggs.

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah *_NAZARIN SHUBUHOHI A KAN AZUMIN "SITTU SHAWWAL"_*

FITOWA TA 1

Almajirin Malik, Yahya bn Yahya Al- Laithiy ya ruwaito wata magana daga Imamu Malik a cikin "Muwatta" wacce Malamai suka fassara ta da cewa; Malik din yana karhanta Azumin kwana shida na watan Shawwal "Sittu Shawwal", alhali an ruwaito hakan daga Annabi (saw). Imamu Muslim ya ruwaito da isnadinsa daga:
ﺳﻌﺪ ﺑﻦ ﺳﻌﻴﺪ ﺑﻦ ﻗﻴﺲ، ﻋﻦ ﻋﻤﺮ ﺑﻦ ﺛﺎﺑﺖ ﺑﻦ ﺍﻟﺤﺎﺭﺙ ﺍﻟﺨﺰﺭﺟﻲ، ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﺃﻳﻮﺏ ﺍﻷﻧﺼﺎﺭﻱ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ، ﺃﻧﻪ
ﺣﺪﺛﻪ، ﺃﻥ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻗﺎﻝ : ‏« ﻣﻦ ﺻﺎﻡ ﺭﻣﻀﺎﻥ ﺛﻢ ﺃﺗﺒﻌﻪ ﺳﺘﺎ ﻣﻦ ﺷﻮﺍﻝ، ﻛﺎﻥ ﻛﺼﻴﺎﻡ
ﺍﻟﺪﻫﺮ ‏» ﺻﺤﻴﺢ ﻣﺴﻠﻢ ‏(/2 822 )
Manzon Allah (S.A.W) ya ce: "Wanda ya azumci Ramadhana, sa'annan ya biyo bayansa da Azumin kwanaki shida na Shawwal, to sakamakonsa kamar Azumin shekara ne".

Yahya Al- Laithiy ya ce: Ya ji Malik yana fadi a game da Azumin "Sittu Shawwal":

ﺇﻧﻪ ﻟﻢ ﻳﺮ ﺃﺣﺪﺍ ﻣﻦ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﻌﻠﻢ ﻭﺍﻟﻔﻘﻪ ﻳﺼﻮﻣﻬﺎ . ﻭﻟﻢ ﻳﺒﻠﻐﻨﻲ ﺫﻟﻚ ﻋﻦ ﺃﺣﺪ ﻣﻦ ﺍﻟﺴﻠﻒ . ﻭﺇﻥ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﻌﻠﻢ ﻳﻜﺮﻫﻮﻥ ﺫﻟﻚ، ﻭﻳﺨﺎﻓﻮﻥ ﺑﺪﻋﺘﻪ. ﻭﺃﻥ ﻳﻠﺤﻖ ﺑﺮﻣﻀﺎﻥ ﻣﺎ ﻟﻴﺲ ﻣﻨﻪ، ﺃﻫﻞ ﺍﻟﺠﻬﺎﻟﺔ ﻭﺍﻟﺠﻔﺎﺀ . ﻟﻮ ﺭﺃﻭﺍ ﻓﻲ ﺫﻟﻚ ﺭﺧﺼﺔ
ﻋﻨﺪ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﻌﻠﻢ . ﻭﺭﺃﻭﻫﻢ ﻳﻌﻤﻠﻮﻥ ﺫﻟﻚ.
ﻣﻮﻃﺄ ﻣﺎﻟﻚ ﺕ ﺍﻷﻋﻈﻤﻲ ‏(/3 447 )

Wannar magana ta Imamu Malik ta kunshi abubuwa kamar haka:

1- A zamaninsa bai ga Malamai masana Fiqhu suna azumtar "Sittu Shawwal" ba.

2- Bai samu riwaya daga Magabata sana yin Azumin ba.

3- Kuma masu Ilimi suna karhanta Azumin saboda abubuwa guda biyu:

a. Suna jin tsoron kar Azumin ya zama kirkirarre ne.

b. Suna jin soron kar jahilai su hada Azumin Ramadhana da waninsa, idan sun ga Malamai suna yinsa.

To, Malamai da suka zo daga baya sun yi nazari a kan wannan magana ta Imamu Malik sun yi ta kokarin fahimtar uzurorinsa, da yin jawabi a kansu, da kuma kokarin ba shi mafita.
Ga nan uzurorin da suka ba shi a takaice kamar haka:

1. Imamu Malik din bai samu Hadisin ba ne.

2. Ko kuma ya samu Hadisin amma bai inganta a wajensa ba.

3. Hadisin ya inganta a wajensa amma Malik ya ji tsoron kar jahilai su hada shi da Ramadhana, don haka za a iya yi a cikin wanin watan Shawwal din.

JAWABI A KAN WADANNAN UZURORI:

Zamu cigaba insha Allahu.

Daga:- Dr. Aliyu Muh'd Sani, Hafizahullah
2018-06-20 19:53 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 18 user
This Week : 41 user
This Month : 28 user
Total all : 270294 visitorsUnited States
LAST PAGES