Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah FA’IDAR YIN AURE DA WURI (02)
Acikin darasinmu na farko kunji yadda Sunnar Magabata take dangane da aurar da ‘Ya’yansu Mata tun kafin ma su balaga. To haka a bangaren ‘Ya’yansu Maza ma. Sukan aurar dasu tun basu wuce shekaru 15 zuwa 18 aduniya ba.
To awannan karon kuma Zauren Fiqhu zai kawo muku Kalamai daga Magabata akan wannan maudhu’in.
1. Wani mutum yace ma Al Ahnafu bn Qays (rah) "Ya kai Baban Bahru, ban ta’ba ganin wani mutum mai tsananin yin abu Sannu-Sannu tamkarka ba".
Sai Ahnafu yace masa "Zaka ga gaggawa gareni cikin abu uku :
1. Sallah da zarar lokacinta yayi, har sai na bada ita.
2. Janazah (Gawa) da zarar an kawota har sai na binneta.
3. ‘Yata da zarar an nemi aurenta, har sai na aurar da ita".
(Aduba MAUSU’ATU IBN ABID DUNYA, juzu’i na 8 shafi na 41).
Kunji iyayen gaske.. Da zarar ‘Ya’yansu sun samu manemi suke aurar dasu.. Amma iyayen yanzu sai kaga mutumin kirki ya fito yana son ‘yarsu amma sai suce wai sai ta gama Makaranta. Wasu ma cewa sukeyi "Ba yanzu zamu aurar da ita ba".
Kuma irin wannan ne yake Qara sanya ya’duwar fasikanci acikin al’ummah. Yarinya tafi shekara biyar da fara yin jinin al’adah, anzo neman aurenta kun Qi bayarwa, to wallahi duk tsiyar da taje ta aikata kuna da babban kamasho acikin duk zunubin da ta kwaso.
Imam Sufyanuth Thauree yana cewa "Hakkin ‘ya’ya akan Mahaifansu shine :
– Su kyautata sunayensu.
– Su ilmantar dasu.
– Su kyautata tarbiyyarsu.
– Suyi musu aure idan sun balaga.
(MAUSU’ATU IBNI ABID DUNYA 8/50).
QATAADAH (rah) wani babban Tabi’iy ne. Yace "Idan har yaro (ko yarinya) ya balaga (ko ta balaga) amma babansa bai aurar dashi ba (ko kuma bai aurar da ita ba) sai yaron (Ko yarinyar) yaje ya aikata alfasha (ko kuma taje ta aikata alfasha) to baban yana da laifi".
(MAUSU’ATU IBN ABID DUNYA 8/50)
To ku iyayen zamani masu dogon buri, kunji maganar gaskiya daga Magabata na kwarai.. Yaro ya gama rika yana yawo zangam-zangam a tsakar gida kun qi kuyi masa aure wai sai yayi degree. Ya gama degree dinma ya nemo aure kunce A’a sai ya samu aiki. Alhali kuma kuna da wadatar da zaku iya ciyar dashi da matarsa kafin ya samu aikin.. Amma kun barshi ya, zama rikakken tuzuru.. To wallahi kuji tsoron Allah. Duniyar nan ba matabbata bace.
Yarinya ta haura shekara 20 agabanku, ta kai yadda zata iya matsuwa da namiji amma kun Qi ku aurar da ita, saboda wai kuna jiran wani Mai kudin ya fito.. Baku samu mai kudin ba, kun sake mayar da ita University wai taje sai tayi Masters.. Wallahi koda ‘yar taku mai tsoron Allah ce wacce ba zata afka cikin alfasha ba, to lallai Kun zalunceta.
Idan kuma ba mai tsoron Allah bace, Ko kuma mai matsananciyar sha’awa ce, to kun jefata cikin hallaka kuma duk abinda ta aikata kuna da zunubi aciki.
Idan zaka aurar da ‘Yarka, ka dubi mutumin kirki mai mutunci ka bashi koda bashi da kudi.
Wani mutum yazo ya tambayi Imam Hasanul Basariy cewa "Hakika ni ina da yarinya budurwa kuma tana da manema. Shin wa ya kamata in aurar ma ita?".
Sai Hasanul Basariy ya bashi amsar cewa "Ka aurar da ita ga mutum mai tsoron Allah. Wanda idan ta kyautata masa zai girmamata. Idan kuma ta munana masa ba zai zalunceta ba".
Amma iyayen yanzu, yawan Kudi shine babban ma’aunin da suka auna samarin ‘ya’yansu dashi, Koda mutum bai damu da addini ba, Koda yana yin zina ko shaye-shaye to zasu bashi ‘yarsu in dai yana da kudi.. (SUBHANALLAH).
Imam Sha’aby yace "Duk wanda ya aurar ma Fasiqi ‘Yarsa, to hakika ya yanke zumuncinsa".
YA ALLAH KA GYARA HALAYENMU KA KYAUTATA LAMURANMU DON HASKEN ALQUR’ANI. AMEEN.
AN GABATAR DA KARATUN A ZAUREN FIQHU 07064213990
2018-02-10 06:15 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 2 user
This Week : 22 user
This Month : 110 user
Total all : 270376 visitors
LAST PAGES

Insane