XtGem Forum catalog

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah *_NAZARIN SHUBUHOHI A KAN AZUMIN "SITTU SHAWWAL"_*

FITOWA TA 2

_JAWABI A KAN WADANNAN UZURORI:_

UZURI NA FARKO: cewa; Imamu Malik bai samu Hadisin ba ne. Ibnul AbdilBarr ya ce:

" ﻟﻢ ﻳﺒﻠﻎ ﻣﺎﻟﻜﺎ ﺣﺪﻳﺚ ﺃﺑﻲ ﺃﻳﻮﺏ ﻋﻠﻰ ﺃﻧﻪ ﺣﺪﻳﺚ ﻣﺪﻧﻲ ﻭﺍﻹﺣﺎﻃﺔ ﺑﻌﻠﻢ ﺍﻟﺨﺎﺻﺔ ﻻ ﺳﺒﻴﻞ ﺇﻟﻴﻪ ." ﺍﻻﺳﺘﺬﻛﺎﺭ ‏(/3 380 ).

Kuma ya ce:

ﻭﻗﺪ ﻳﻤﻜﻦ ﺃﻥ ﻳﻜﻮﻥ ﺟﻬﻞ ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ ﻭﻟﻮ ﻋﻠﻤﻪ ﻟﻘﺎﻝ ﺑﻪ ﻭﺍﻟﻠﻪ ﺃﻋﻠﻢ.
ﺍﻻﺳﺘﺬﻛﺎﺭ ‏(/3 380 )

Amma kuma sai dai maganar Malik din tana nuna Malik din ya san da Hadisin. Shi ya sa Ibnu AbdilBarr ya dawo ya ce:

ﻭﻣﺎ ﺃﻇﻦ ﻣﺎﻟﻜﺎ ﺟﻬﻞ ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ ﻭﺍﻟﻠﻪ ﺃﻋﻠﻢ ﻷﻧﻪ ﺣﺪﻳﺚ ﻣﺪﻧﻲ ﺍﻧﻔﺮﺩ ﺑﻪ ﻋﻤﺮ ﺑﻦ ﺛﺎﺑﺖ ﻭﻗﺪ ﻗﻴﻞ ﺇﻧﻪ ﺭﻭﻯ ﻋﻨﻪ ﻣﺎﻟﻚ ﻭﻟﻮﻻ ﻋﻠﻤﻪ ﺑﻪ ﻣﺎ ﺃﻧﻜﺮﻩ.
ﺍﻻﺳﺘﺬﻛﺎﺭ ‏(/3 380 )

Don haka kawai shi dai ya bar Hadisin ne saboda bai samu magabata sun yi aiki da shi ba. Kuma da ma an san cewa; aikin magabata - musamman mutanen garin Madina - asali ne a Fiqhun Imamu Malik.

UZURI NA BIYU: amma magana a kan rashin ingancin Hadisin a wajensa kuwa, kamar yadda AbdilBarr ya ce:

ﻭﺃﻇﻦ ﺍﻟﺸﻴﺦ ﻋﻤﺮ ﺑﻦ ﺛﺎﺑﺖ ﻟﻢ ﻳﻜﻦ ﻋﻨﺪﻩ ﻣﻤﻦ ﻳﻌﺘﻤﺪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﻗﺪ ﺗﺮﻙ ﻣﺎﻟﻚ ﺍﻻﺣﺘﺠﺎﺝ ﺑﺒﻌﺾ ﻣﺎ ﺭﻭﺍﻩ ﻋﻦ ﺑﻌﺾ
ﺷﻴﻮﺧﻪ ﺇﺫﺍ ﻟﻢ ﻳﺜﻖ ﺑﺤﻔﻈﻪ ﺑﺒﻌﺾ ﻣﺎ ﺭﻭﺍﻩ. ﺍﻻﺳﺘﺬﻛﺎﺭ ‏(/3 380 )

Da kuma kasancewar an yi magana a kan wani maruwaici mai suna Sa'ad bn Sa'eed, a cikin Isnadin Hadisin na Abu Ayyub Al- Ansariy (ra) a wajen Muslim, to za a iya ba da amsa ta fuskoki kamar haka:

1. Hadisin a matsayin Mutawatiri yake, saboda an ruwaito shi daga Sahabbai goma sha biyu (12), wato: Abu Ayyub, Thauban, Jabir, Abu Huraira, Ibnu Abbas, Ibnu Umar, Gannam, Bara'u, Shaddad, Aus, Anas da A'isha (ra).

Al- Gumariy ya ce:
ﻭﺭﺩ ﻣﻦ ﺣﺪﻳﺚ ﺃﺑﻲ ﺃﻳﻮﺏ، ﻭﺛﻮﺑﺎﻥ ﻭﺟﺎﺑﺮ، ﻭﺃﺑﻲ ﻫﺮﻳﺮﺓ، ﻭﺍﺑﻦ ﻋﺒﺎﺱ، ﻭﺍﺑﻦ ﻋﻤﺮ، ﻭﻏﻨﺎﻡ، ﻭﺍﻟﺒﺮﺍﺀ ﺑﻦ ﻋﺎﺯﺏ،
ﻭﺷﺪﺍﺩ ﺑﻦ ﺃﻭﺱ، ﻭﺃﻭﺱ ﺑﻦ ﺃﻭﺱ، ﻭﺃﻧﺲ. ﺍﻟﻬﺪﺍﻳﺔ ﻓﻲ ﺗﺨﺮﻳﺞ ﺃﺣﺎﺩﻳﺚ ﺍﻟﺒﺪﺍﻳﺔ ‏(/5 209 - 212 )

Sai kuma ya kawo Malaman da suka fitar da Hadisin kowanne a cikinsu.

Al- Mubarakaforiy ya ce:
ﻭﺃﻣﺎ ﺣﺪﻳﺚ ﻋﺎﺋﺸﺔ ﻓﺮﻭﺍﻩ ﺍﻟﻄﺒﺮﺍﻧﻲ ﺃﻳﻀﺎ ﻛﺬﺍ ﻓﻲ ﺍﻟﻤﺮﻗﺎﺓ.
ﺗﺤﻔﺔ ﺍﻷﺣﻮﺫﻱ ‏(/3 388 )

Saboda haka Hadisi ne da ya kai matsayin Mutawatiri, wanda ya tabbata ta hanyar yakini ba zato ba, balle a yi shakka a kan ingancinsa.

2. Amma Hadisin Abu Ayyub (ra) wanda Muslim ya ruwaito, wanda a cikin Isnadinsa akwai Sa'ad bn Sa'eed, Malamai sun yi magana a kan haddarsa, sun tabbatar da cewa yana da rauni.

Nasa'iy ya ce:
ﺳﻌﺪ ﺑﻦ ﺳﻌﻴﺪ ﺿﻌﻴﻒ، ﻛﺬﻟﻚ ﻗﺎﻝ ﺃﺣﻤﺪ ﺑﻦ ﺣﻨﺒﻞ : ﻭﻫﻢ ﺛﻼﺛﺔ ﺇﺧﻮﺓ ﻳﺤﻴﻰ ﺑﻦ ﺳﻌﻴﺪ ﺑﻦ ﻗﻴﺲ ﺍﻟﺜﻘﺔ ﺍﻟﻤﺄﻣﻮﻥ ﺃﺣﺪ ﺍﻷﺋﻤﺔ، ﻭﻋﺒﺪ ﺭﺑﻪ ﺑﻦ ﺳﻌﻴﺪ ﻻ ﺑﺄﺱ ﺑﻪ، ﻭﺳﻌﺪ ﺑﻦ ﺳﻌﻴﺪ ﺛﺎﻟﺜﻬﻢ ﺿﻌﻴﻒ. ﺍﻟﺴﻨﻦ ﺍﻟﻜﺒﺮﻯ ﻟﻠﻨﺴﺎﺋﻲ ‏(/3 240 ).

Amma sai dai an yi masa "Mutaba'a" har guda hudu:

1. Mutaba'a daga Safwan bn Sulaim:
ﻋﻦ ﺻﻔﻮﺍﻥ، ﻭﺳﻌﺪ ﺑﻦ ﺳﻌﻴﺪ، ﻋﻦ ﻋﻤﺮ ﺑﻦ ﺛﺎﺑﺖ، ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﺃﻳﻮﺏ، ﻋﻦ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻗﺎﻝ : ‏« ﻣﻦ
ﺻﺎﻡ ﺭﻣﻀﺎﻥ ﺛﻢ ﺃﺗﺒﻌﻪ ﺳﺘﺔ ﻣﻦ ﺷﻮﺍﻝ، ﻓﺬﻟﻚ ﺻﻴﺎﻡ ﺍﻟﺪﻫﺮ ‏». ﺳﻨﻦ ﺃﺑﻲ ﺩﺍﻭﺩ ﺕ ﺍﻷﺭﻧﺆﻭﻁ ‏(/4 98 ‏) ، ﺳﻨﻦ ﺍﻟﺪﺍﺭﻣﻲ ‏(/2 1100 - 1101 ‏) ، ﺻﺤﻴﺢ ﺍﺑﻦ ﺧﺰﻳﻤﺔ ﻁ 3 ‏(/2 1014 ‏) ، ﺻﺤﻴﺢ ﺍﺑﻦ ﺣﺒﺎﻥ - ﻣﺤﻘﻘﺎ ‏(/8 397 ‏) ، ﺍﻟﺴﻨﻦ ﺍﻟﻜﺒﺮﻯ ﻟﻠﻨﺴﺎﺋﻲ ‏(/3 239 ).

2. Mutaba'a daga dan uwansa Abdurabbihi bn Sa'eed, Nasa'iy ya ruwaito:
ﻋﻦ ﻋﺒﺪ ﺭﺑﻪ ﺑﻦ ﺳﻌﻴﺪ، ﻋﻦ ﻋﻤﺮ ﺑﻦ ﺛﺎﺑﺖ، ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﺃﻳﻮﺏ ﺍﻷﻧﺼﺎﺭﻱ، ﺃﻧﻪ ﻗﺎﻝ : ‏«ﻣﻦ ﺻﺎﻡ ﺷﻬﺮ ﺭﻣﻀﺎﻥ ﺛﻢ
ﺃﺗﺒﻌﻪ ﺳﺘﺔ ﺃﻳﺎﻡ ﻣﻦ ﺷﻮﺍﻝ ﻓﻜﺄﻧﻤﺎ ﺻﺎﻡ ﺍﻟﺴﻨﺔ ﻛﻠﻬﺎ ‏». ﺍﻟﺴﻨﻦ ﺍﻟﻜﺒﺮﻯ ﻟﻠﻨﺴﺎﺋﻲ ‏(/3 240 ).

3. Mutaba'a daga dan uwansa Yahya bn Sa'eed, Nasa'iy ya ruwaito:
ﻋﻦ ﻳﺤﻴﻰ ﺑﻦ ﺳﻌﻴﺪ، ﻋﻦ ﻋﻤﺮ ﺑﻦ ﺛﺎﺑﺖ، ﻗﺎﻝ : ﻏﺰﻭﻧﺎ ﻣﻊ ﺃﺑﻲ ﺃﻳﻮﺏ ﻓﺼﺎﻡ ﺭﻣﻀﺎﻥ ﻭﺻﻤﻨﺎ، ﻓﻠﻤﺎ ﺃﻓﻄﺮﻧﺎ، ﻗﺎﻡ ﻓﻲ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻓﻘﺎﻝ : ﺇﻧﻲ ﺳﻤﻌﺖ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻳﻘﻮﻝ : ‏« ﻣﻦ ﺻﺎﻡ ﺭﻣﻀﺎﻥ ﻭﺻﺎﻡ ﺳﺘﺔ ﺃﻳﺎﻡ ﻣﻦ ﺷﻮﺍﻝ ﻛﺎﻥ ﻛﺼﻴﺎﻡ ﺍﻟﺪﻫﺮ ‏»
ﺍﻟﺴﻨﻦ ﺍﻟﻜﺒﺮﻯ ﻟﻠﻨﺴﺎﺋﻲ ‏(/3 240 ).

4. Mutaba'a daga Usman bn Amr, Nasa'iy ya ruwaito:
ﻋﻦ ﻋﺜﻤﺎﻥ ﻭﻫﻮ ﺍﺑﻦ ﻋﻤﺮﻭ ﺍﻟﺤﺮﺍﻧﻲ ﻗﺎﻝ : ﺣﺪﺛﻨﺎ ﻋﻤﺮ ﻳﻌﻨﻲ ﺍﺑﻦ ﺛﺎﺑﺖ، ﻋﻦ ﻣﺤﻤﺪ ﺑﻦ ﺍﻟﻤﻨﻜﺪﺭ، ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﺃﻳﻮﺏ
ﺍﻷﻧﺼﺎﺭﻱ، ﻗﺎﻝ : ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ، ﻧﺤﻮﻩ. ﺍﻟﺴﻨﻦ ﺍﻟﻜﺒﺮﻯ ﻟﻠﻨﺴﺎﺋﻲ ‏(/3 241 ).

Saboda haka raunin Sa'ad bn Sa'eed ba matsala ba ne wajen tabbatar Hadisin.

Wannan a takaice kenan.
Saboda haka Hadisin ya tabbata. Don haka rashin azumtar "Sittu Shawwal" a wajen Magabata, bisa tsoron kar ya zama kirkirarre ba hujja ba ne da zai hana aiki da Hadisin, saboda matukar Hadisi ya tabbata daga Manzon Allah (S.A.W) to ya halasta a yi aiki da shi.

Al- Baihaqiy ya ce:
ﻭﻣﺬﻫﺐ ﺍﻟﺸﺎﻓﻌﻲ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﻣﺘﺎﺑﻌﺔ ﺍﻟﺴﻨﺔ ﺇﺫﺍ ﺛﺒﺘﺖ، ﻭﻗﺪ ﺛﺒﺘﺖ ﻫﺬﻩ ﺍﻟﺴﻨﺔ. ﻣﻌﺮﻓﺔ ﺍﻟﺴﻨﻦ ﻭﺍﻵﺛﺎﺭ ‏(/6 380 ).

Al- Nawawiy ma ya ce:
ﻭﺇﺫﺍ ﺛﺒﺘﺖ ﺍﻟﺴﻨﺔ ﻻ ﺗﺘﺮﻙ ﻟﺘﺮﻙ ﺑﻌﺾ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺃﻭ ﺃﻛﺜﺮﻫﻢ ﺃﻭ ﻛﻠﻬﻢ ﻟﻬﺎ ﺷﺮﺡ ﺍﻟﻨﻮﻭﻱ ﻋﻠﻰ ﻣﺴﻠﻢ ‏(/8 56 ).

Wannan in an sallama a kan cewa; Magabata ba su yi "Sittu Shawwal" ba kenan, alhali an samu Magabata suna yi kamar yadda ya zo a wadannan riwayoyi kamar haka:

1. Daga Hasanul Basariy, ya rasu (110).
ﻋﻦ ﺍﻟﺤﺴﻦ، ﻗﺎﻝ : ﺇﺫﺍ ﺫﻛﺮ ﻋﻨﺪﻩ ﺳﺘﺔ ﺃﻳﺎﻡ ﺍﻟﺘﻲ ﻳﺼﻮﻣﻬﺎ ﺑﻌﺾ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺑﻌﺪ ﺭﻣﻀﺎﻥ ﺗﻄﻮﻋﺎ، ﻛﺎﻥ ﻳﻘﻮﻝ : ‏«ﻟﻘﺪ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻬﺬﺍ ﺍﻟﺸﻬﺮ ﻟﻠﺴﻨﺔ ﻛﻠﻬﺎ ‏».
ﻣﺼﻨﻒ ﺍﺑﻦ ﺃﺑﻲ ﺷﻴﺒﺔ ‏(/2 342 ).

2. Daga Ma'amar bn Rashid, ya rasu (153).
ﻗﺎﻝ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﺮﺯﺍﻕ : ﻭﺳﺄﻟﺖ ﻣﻌﻤﺮﺍ ﻋﻦ ﺻﻴﺎﻡ ﺍﻟﺴﺖ ﺍﻟﺘﻲ ﺑﻌﺪ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻔﻄﺮ، ﻭﻗﺎﻟﻮﺍ ﻟﻪ : ﺗﺼﺎﻡ ﺑﻌﺪ ﺍﻟﻔﻄﺮ ﺑﻴﻮﻡ، ﻓﻘﺎﻝ : ‏« ﻣﻌﺎﺫ ﺍﻟﻠﻪ ﺇﻧﻤﺎ ﻫﻲ ﺃﻳﺎﻡ ﻋﻴﺪ ﻭﺃﻛﻞ ﻭﺷﺮﺏ، ﻭﻟﻜﻦ ﺗﺼﺎﻡ ﺛﻼﺛﺔ ﺃﻳﺎﻡ ﻗﺒﻞ ﺃﻳﺎﻡ ﺍﻟﻐﺮ، ﺃﻭ ﺛﻼﺛﺔ ﺃﻳﺎﻡ ﺍﻟﻐﺮ ﺃﻭ ﺑﻌﺪﻫﺎ، ﻭﺃﻳﺎﻡ ﺍﻟﻐﺮ ﺛﻼﺛﺔ ﻋﺸﺮ، ﻭﺃﺭﺑﻌﺔ ﻋﺸﺮ، ﻭﺧﻤﺴﺔ ﻋﺸﺮ ‏». ﻣﺼﻨﻒ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﺮﺯﺍﻕ ﺍﻟﺼﻨﻌﺎﻧﻲ ‏(/4 316 ).

Wadannan biyun sun gabaci Imamu Malik.

3. Daga Abdullahi bnl Mubarak, ya yi zamani da Malik, ya rasu (181).
ﻭﻗﺪ ﺭﻭﻱ ﻋﻦ ﺍﺑﻦ ﺍﻟﻤﺒﺎﺭﻙ ﺃﻧﻪ ﻗﺎﻝ : ‏«ﺇﻥ ﺻﺎﻡ ﺳﺘﺔ ﺃﻳﺎﻡ ﻣﻦ ﺷﻮﺍﻝ ﻣﺘﻔﺮﻗﺎ ﻓﻬﻮ ﺟﺎﺋﺰ ‏». ﺳﻨﻦ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ ﺕ ﺷﺎﻛﺮ ‏(/3 124 ).
Saboda haka wadannan riwayoyi suna nuna cewa; Magabata sun san da Hadisin, kuma sun yi aiki da shi.

UZURI NA UKU: Imamu Malik ya karhanta Azumin ne saboda tsoron kar Jahilai su cakuda tsakanin Azumin Ramadhan da waninsa, har a kasa banbancewa. Ibnu AbdilBarr ya ce:
ﺍﻟﺬﻱ ﻛﺮﻫﻪ ﻟﻪ ﻣﺎﻟﻚ ﺃﻣﺮ ﻗﺪ ﺑﻴﻨﻪ ﻭﺃﻭﺿﺤﻪ ﻭﺫﻟﻚ ﺧﺸﻴﺔ ﺃﻥ ﻳﻀﺎﻑ ﺇﻟﻰ ﻓﺮﺽ ﺭﻣﻀﺎﻥ ﻭﺃﻥ ﻳﺴﺘﺒﻴﻦ ﺫﻟﻚ ﺇﻟﻰ ﺍﻟﻌﺎﻣﺔ ﻭﻛﺎﻥ - ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ - ﻣﺘﺤﻔﻈﺎ ﻛﺜﻴﺮ ﺍﻻﺣﺘﻴﺎﻁ ﻟﻠﺪﻳﻦ. ﺍﻻﺳﺘﺬﻛﺎﺭ ‏(/3 380 ).

To, wannan kawai Istihsani ne da taka tsam-tsam daga Imamu Malik, amma kuma ba lallai ne a samu hakan ba, saboda ranar Eidi tana raba tsakanin Azumin Ramadhan da waninsa.
Musamman a irin wannan zamani da za ka samu mafi yawan mutane a karshen watan Shawwal din suke yin Azumin, wasu masu yawa kuma a tsakiyarsa, 'yan kadan ne masu yi a farkon watan kai tsaye bayan ranar Eidi.

Don haka tsoron kar jahilai su riskar da "Sittu Shawwal" da Azumin Ramadhana ba hujja ba ne na hana yin Azumin "Sittu Shawwal" din gaba daya da karhanta shi.

Za mu takaita a nan, Insha Allahu za mu cigaba da nazari a kan shubuhar cewa; Hadisin bai tabbata ba, saboda akwai gwaranci a cikinsa.

Daga:- Dr. Aliyu Muh'd Sani, Hafizahullah
2018-06-20 20:02 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 25 user
This Week : 48 user
This Month : 35 user
Total all : 270301 visitorsUnited States
LAST PAGES