Snack's 1967

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah 005 AURE KO MAKARANTA?

Wallafar: *Shaikh Muhammad Abdullah Assalafiy*
Rubutu na 5
Daga: *zauren majlisin sunnah*
*GYARA TUNANI*
62. Ko kuna tsammanin muna ƙyamar ilimin bokon mace ne?
63. Ba ku san mun san cewa: Mata su ne kashin bayan rayuwa ba?
64. Ba ku san mun san cewa: Mata da ’ya’ya su ne mafiya soyuwan mutane a wurin Annabin Rahama (SAAS) ba?
65. Amma kuma ba ku san duk da haka, ya nuna cewa: Mata sun fi yawa a cikin Wutar Lahira ba?
66. Ba ku san mun fi kowa son ganin gyaruwa da daidaituwar al’amuran mata ba?
67. Ba ku san cewa mu ma mun yi karatun bokon, kuma mun san irin alfanu ko rashin alfanunsa ba?
68. Ba ku san mun san cewa: Ilmantar da mace kamar ilmantar da duniya ce ba?
69. Amma ina amfanin ilimi in babu tarbiyya da kyawawan ɗabi’u da halaye?
70. Ko kuwa ina amfanin ilimin da zai kai mace ga karewa a cikin Wuta a Lahira?
71. Yaushe za a iya samun nagartaccen ilimi ba tare da natsuwar zuciya da kwanciyar hankali ba?
72. Ashe aure ba shi ne cikakkiyar hanyar samun wannan natsuwar da kwanciyar hankalin ga matasa ba?
73. Yanzu daliba ba za ta iya yin karatun boko tare da aurenta ba?
74. Samun juna-biyu a yau a wurin ma’aurata, ba sai da yarda kuma da ganin-damarsu ba?
75. Ko kuwa kun yarda ne da zancen masu cewa: Aure da wuri yana da hatsari?!
76. Kun amince ne da tatsuniyar masu son rage al’ummar musulmi?
77. Kun yi watsi ne da koyarwar addininku da kyawawan al’adunku?
78. Wannan watsin ba shi ne ummul habaa’isin aukuwan wahalhalu da masifu a cikinmu ba?
*MAFITA GUDA*
79. Shin menene amfanin yawan jama’ar musulmi a ƙasar nan?
80. Shin menene amfanin tarin dukiyoyin jama’ar musulmi a ƙasar nan?
81. Shin menene amfanin ƙarfin mulkin jama’ar musulmi a ƙasar nan?
82. Yanzu musulmi ba za ku iya gyara tsarin koyarwa a makarantun bokon maza da mata ba?
83. Yanzu ba za ku iya gyara makarantun bokon su dace da yadda addininku da kyawawan al’adunku su ke ba?
84. Yanzu musulmi ba za ku iya gyara tsarin karatun bokon ya dace da ƙa’idojin addininku da kyawawan al’adunku ba?
85. Yanzu musulmi ba za ku iya samar da makarantun bokon da suka dace da mata ma’aurata ba?
86. In kuwa haka ne, to ina amfanin iliminku, ya ku musulmi!?
87. In kuma haka ne, ina amfanin albarkar yawanku, ya ku musulmi!?
88. Sannan kuma in haka ne, menene amfanin rayuwarku, ya ku jama’ar musulmi!?
89. Menene amfanin rayuwa a cikin wulaƙanci da ƙaskanci da rashin ’yancin yin addini?
Dan uwanku: *Muneer Yusuf Assalafy*
2017-12-14 12:38 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 50 user
This Week : 50 user
This Month : 1003 user
Total all : 271269 visitorsUnited States
LAST PAGES