XtGem Forum catalog

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah AL'UMMARMU TA PLATEAU LALLE NE A KARA HIMMA DOMIN GINA KASA DA AL'UMMAH:
1. A daliban da aka dauka bana 2018 a Nigerian Defence Academy (NDA) da ke Kaduna, daga Jihar Plateau mutum 50 ne daidai, to amma a cikin su 50 din mutum bakwai (7) ne kacal ke dauke da suna irin na Musulmi! Mutum bakwai din nan su ne kawai Musulmi daga dukkan tsangayoyin Jami'ar guda hudu: Faculty of Arts and Social Science. Faculty of Engineering. Faculty of Science. Faculty of Military Science and Interdisciplinary Studies! Lalle wannan abin takaici ne matuka.
2. Lalle muna sane da irin tarbiyyar da kungiyar CAN ta dora kiristocin Nigeria a kanta shekara da shekaru na share al'ummar Musulmi daga dukkan wani hakki nasu mai amfanarwa; wanda wannan ya sa a duk inda su kiristoci suke mulki, ko suka sami wata dama to sai ka ga tasirin wannan muguwar tarbiyya ta kungiyar CAN daga gare su, lalle muna sane da wannan hakika, to amma wajibi ne a kan Al'ummah a duk inda suke su dage su yi kokari domin kauda ko wane irin zalunci ne daga kansu, a ta hanyar ka'ida, da bin doka da oda.
3. Gaskiyan al'amari shi ne Musulmi suna da yawan gaske a Jihar Plateau; domin akwai kananan hukumomi da dama a cikin Jihar wadanda Musulmi su ne masu rinjaye a cikinsu; misali: Jos-North, Wase, Kanam. Sannan kuma akwai wadanda suke ana rabi-da-rabi ne a cikinsu, kamar su: Qua'an Pan, Mangu, Shendam, Barikinladi...
4. Kiranmu dai ga Al'ummah shi ne kada su mika wuya ga waaqi'in zalunci, a'a su kara tashi tsaye domin dawo da hakkokinsu ta hanyar da ba ta saba wa Shari'ah ba; domin tabbatar da maslahar kasarsu da al'ummarsu. Allah Ya taimake mu. Ameen.
2018-06-30 05:17 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 11 user
This Week : 67 user
This Month : 54 user
Total all : 270320 visitorsUnited States
LAST PAGES