Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah AN KAFA KUNGIYAR IZALA NE SABODA TSAIDA SUNNA DA KAUDA BIDI'A:
1. An kafa Kungiyar Izala ne domin a kira al'ummar Musulmi su tsaida sunnar Annabi mai tsira da amincin Allah cikin Aqida, da Ibada, da Mu'amala, su kuma guje wa bidi'a cikin Aqida, da Ibada, da Mu'amala iya iyawarsu.
2. Wajibi ne membobin Kungiyar Izala a duk inda suke su tafi a kan wannan manufa har abada, kada tsawaitar lokaci ya raba su da wannan kyakkyawar manufa, ba daidai ba ne wani ya bar yin aiki da tabbatacciyar Sunna cikin mas'alar Aqida, ko Ibada, ko Mu'amala a bisa hujjar cewa ta saba wa wata mazhaba daga cikin mazhabobin fiqhu da ake da su a fage.
3. Lalle ba a kafa Kungiyar Izala a kan wata mazhaba daga cikin mazhabobi ba sawaa'un Hanafiyyah ce, ko Malikiyyah, ko Shafi'iyyah, ko Hambaliyyah, ko Zahiriyyah ko ma wanin wadannan; wannan shi ne ya sa ma ba a ambaci sunan wata mazhaba ba a cikin constitution din Kungiyar, illa dai Alkur'ani da Hadithi da Ijma'i.
4. A inda duk wata mazhaba ta dace da Alkur'ani da Hadithi da Ijma'i, to lalle kungiyar Izalah tana tare da ita a nan, a inda kuma ta saba wa Alkur'ani da Hadithi da Ijma'i to lalle kungiyar Izalah ba ta tare da ita a nan; wannan kuwa shi ne aqidar ko wane musulmin kirki tun daga zamanin Sahabbai har zuwa karshen Duniya.
5. Abin takaici ne matuka wasu su rika cewa: an kafa kungiyar Izala ne a kan mazhabar Malikiyya, maimakon a bin da aka rubuta a cikin constitution dinta na cewa an kafa ta ne a kan Alkur'ani da Hadithi da Ijma'i!
6. Allah Ka taimake mu Ka cusa son yin aiki da ingantacciyar sunnar ManzonKa a cikin zukatansu. Ameen.
2018-03-31 21:57 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 30 user
This Week : 53 user
This Month : 40 user
Total all : 270306 visitorsUnited States
LAST PAGES

The Soda Pop