Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah BIRI YAYI KAMA DA MUTUM
Dr. Mansur Sakkwato
.
A gaskiya ban taba gaskata zargin da ake yi ma Prof. Maqary na Shi’anci ba a lokacin da na ji ana yayata shi a Social Media. Amma wannan clip nasa ya ba ni mamaki matuka.
– Ba ina maganar kurakuran larabcin da ya yi a cikin karanta Hadisin Muslim ba. Ba ni mamakin Malamin Arabiya zalla in ya kasa karanta larabcin Hadisi.
– Ba ina maganar kalmar (minal bayyinati) da ya kara a cikin ayar suratu Áli Imrana ba. Malaman Arabiyya zalla Qur’ani ya fi komai ba su wahala.
Ni abubuwa biyar ne a cikin wannan clip suka ba ni mamaki duk da gajarcinsa:
1- Fifita falalar Sayyidina Ali ® a kan sauran Sahabbai. Alhalin duk musulmi – in ban da yan Shi’a – sun hadu a kan cewa, shi ne na hudu a musulunci, kuma halifofi uku sun fi shi girman falala da daraja. Daman kuma a nan ne asalin sabanin yan Shi’a da sauran musulmi yake.
2. Hadisin kallon sayyidina Aliyu ibada ne. Sarkin Malaman Hadisi Imamuz Zahaby ya ce karya ne, wani dan Shi’a wai shi Gumari ya ce a’a gaskiya ne a wurinsu. Amma Prof ya karbi maganar dan Shi’a ya ture ta Imamuz Zahaby.
3- Zargin wasu Ahlus Sunnah da kin sayyidina Ali ko rashin son bayyana darajojinsa. Ba mu san a doron kasa akwai wani mai kiran kansa Ahlus Sunnah kuma yana kin sayyidina Ali ko yana jin haushinsa ba. Wannan kagen yan Shi’a ne kawai Prof ya kwaso.
4- Kokarin Prof na raunata hadisin da ya ce ayi riko da littafin Allah da Sunnar Manzonsa wanda ya zo a littafan Hadisi manya ta hanyar Sahabbai da yawa irin su: Sayyidina Umar da dansa Abdullahi da Ibnu Abbas da Abu Sa’id Al-khudry da Abu Huraira da Anas da Abdullahi bn Abi Najih da Amru bn Auf Al-muzani da Sahabbai dama kuma malamai suka tabbatar da ingancinsa.
5- Prof yana ta kokarin nuna yana cikin Ahlus Sunnah amma kuma ya cire Matan Manzon Allah (S) daga cikin iyalansa. Ban san wani Ahlus Sunnah a duniya da ya ce matan Manzon Allah (S) ba su cikin iyalansa ba. Sai dai yan Shi’a.
A takaice, hawa da gangarar wa’azin Prof da kwatanta shi da wa’azin almajiran Zakzaky wadanda suke taqiyya zai sa mutum ya ce, lallai: Biri ya yi kama da mutum.
Allah ya shirya al’umma ya kare mu daga masu gurbata addini a cikin rigar malanta.
2018-06-19 09:25 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 10 user
This Week : 81 user
This Month : 68 user
Total all : 270334 visitors
LAST PAGES

Polly po-cket