Old school Easter eggs.

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah FASSARAR KHUDBAR JUMU’AH DAGA MASJID ABI HURAIRAH DAKE TSAFE ZAMFARA
DAGA IBRAHIM RABILU TSAFE
A wannan makon limam Sani Abi hurairah Tsafe ya gabatar da khudbar ne akan #MUHIMMANCIN_NAFILAH
Bayan mukaddimah……
Yan uwa musulmi masu albarka hakika gaskiyar zance shine Alqur’ani Mai tsarki, Mafi kyawun shiriya itace shiriya ta Annabi Muhammadu sallal lahu alaihi wassalam, Mafi sharrin ayyuka shine kirkirar abu ga addini.
Yan uwa musulmi masu albarka ina maku Nasiha tare da ni kaina da muji tsoron ALLAH domin jin tsoron ALLAH shine jagora ga rayuwar mu, ALLAH yana fada cikin suratul kasas cewa “WANNAN GIDAN NA LAHIRA MU SANYA SHINE GA MASU TSORON ALLAH HAKIKA AQIBA MAI KYAU ITA KUWA AQIBA MAI KYAU TANA GA MASU TSORON ALLAH”
Saboda kaunar da ALLAH keyi mana ya sanya mana abubuwa da Zamu amfana dasu, kamar nafilfili da sauransu, Nafila ta sallah tana Matukar muhimmancin ga ibada,
Yan uwa musulmi masu albarka sallah itace abunda za’a fara bincike a gobe Kiyama, Manzo sallal lahu alaihi wassalam na cewa “Farkon abunda za’a yiwa dan Adam hisabi akanshi shine sallah idan tayi kyau to dan Adam ya dace idan kuma an samu matsala sai ALLAH ya umarci mala’iku su binciki shin akwai nafila?
Idan akwai to sai ayi amfani da ita wajen cike sallar farilla”
Haka ma a azumi da zakkah sai a diba idan akwai wakafi da sauran ibadu!!
Kenan koda a wannan hadisin muka tsaya lallai zamu fahimci cewa nafila nada matukar muhimmanci.
A wajen yin ibadar sallah ana bukatar natsuwa sosai Ibn Abbas ya ruwaito yace” Sai kana da natsuwa sannan sallahr ka zata karbu ”
Yan uwa musulmi masu albarka yawan yin nafila yana sa mutun yazama abokin Manzo sallal lahu alaihi wassalam a gidan aljannah
Akwai wani sahabin Manzo sallal Sallal lahu alaihi wassalam idan Annabi zai yi alwala sai sahabin ya dauki talkaman Annabi ya rike a hannunsa hakama idan Manzo sallal lahu alaihi wassalam zai yi sallah yakan tsaya har sai Annabi ya fito, Wata rana sai Manzo sallal lahu alaihi wassalam ya tambaye shi mi kake bukata inyi maka??
Sai yace ina so in zama abokin ka a gidan aljannah…..
Sai Manzo sallal lahu alaihi wassalam yace to ka taimake ni da yin nafila a koda yaushe. ”
Yan uwa musulmi masu albarka yawaita nafila na kara kusan tar da dan Adam ga ubangiji, ALLAH madaukakin sarki na cewa” BAWA BAZAI GUSHE YANA SUJJADAH HAR SAI NA SOSHI ”
Yan uwa musulmi masu albarka yawaita yin nafila kara maka kusanci da ubangiji ALLAH
Abdullahi bn Umar ya ruwaito cewa” Kafin sallar azahar kayi raka’a 2 bayan sallar kuma kayi 2 la’asar kayi 2 bayan ta kayi 2 hakama a magrib da isha’i hakama a sallar asuba kafin ta wato sallar fajir ”
Haka ma Manzo sallal lahu alaihi wassalam yace” Duk wanda yake yawaita yin nafila raka’a 12 a rana ALLAH zai gina mashi gida a aljannah ”
Haka ma Manzo sallal lahu alaihi wassalam yana cewa” Kuyi raka’a 2 kafin magrib ya fadi haka har sau uku amma ga wanda yake sa hali ”
Haka ma Aisha radiyyallahu anha ta ruwaito cewa” Manzo sallal lahu alaihi wassalam bai taba barin nafila ba a lokachin sallar asuba ba ”
Yan uwa musulmi masu albarka hadisin dake magana game da ba’a sallah bayan la’asar na nufin idan an dade da gama sallar ne.
Daga cikin nafilolin da ake bukatar yawaita aikatawa akwai sallar duha wato ita anayi ta ne da safe, Manzo sallal lahu alaihi wassalam yace “Dan Adam yana da gabobi guda 360 ana bukatar a kullum kabada Sadaka kwatan kwacin haka sai sahabbai suka ce to idan baka da kudin bada Sadakar?? Sai Manzo sallal lahu alaihi wassalam yace to ka tsaftace massallaci (kamar shara ko kuma dauke wani tsinke) koda ma ace ka gaza haka to kayi sallar duha ”
Yan uwa musulmi masu albarka hakika addinin musulunci yana da Matukar dadi da kuma garabasa ga wani hadisi daga Manzo sallal lahu alaihi wassalam cewa
” Duk wanda ya fito daga gida yayi aikatawa zaije massallaci to ana rubuta mashi ladar aikin hajji da umrah ”
Hakika yan uwa musulmi idan muka yawaita yin nafila za’a rubuta sunayen mu cikin illiyun
Yan uwa musulmi bayan sallar asuba yana da kyau mu rika zaunawa koda awa guda ko biyu ne Muna yin tasbih domin falalar dake ciki, Hadisi daga Manzo sallal lahu alaihi wassalam na cewa “Bayan kammala sallar asuba ka zauna har rana ta fito kana da ladar aikin hajji cikakke cikakke cikakke!!
Yan uwa musulmi dole ne mu rage yawan zama ana hira ana surutu fiye da awa guda alhali zaman baida wani amfani garemu,
Imam Muslim ya ruwaito daga Manzo sallal lahu alaihi wassalam cewa “Dayanku bazai yi alwala yana jiran sallah ba face wuta ta haramta gareshi!!”
Yan uwa musulmi kunji falala mai kyau kenan masu zuwa massallaci da Wuri suna jiran limam sun samu shiga a wannan.
Sannan kuma yan uwa musulmi yana da kyau mu yawaita yin nafila a gidajen mu domin Manzo sallal lahu alaihi wassalam yace “Kada mu maida gidajen mu kamar makabartu (Domin ba’a sallah a makabarta)
Manzo sallal lahu alaihi wassalam yace” Mafificin nafila itace nafillar da akayi a gida ”
Yan uwa musulmi kada mu rangwantar da kawunan mu mu kashe jikin mu da hira da surutai marar sa amfani domin wallahi akwai ranar da Zamu nemi ina ma ace Zamu yi aiki koda na kwayar zarra ne!!
Akwai falala mai yawa a cikin sallar nafila, Manzo sallal lahu alaihi wassalam “SALLAR fajir (Kafin asuba) tafi duniya da abunda ke cikin ta”
To yan uwa musulmi kunji fa……
Tabi’ai da sahabbai sun kasance idan wani yayi laifi yana zuwa yayi nafila ya roki Allah ya gafarta masa.
*Sallar nafila tana daga Darajar dan Adam a wurin ALLAH
Hakika sahabbai da Tabi’ai suna yawaita yin nafila domin tsannanin koyi da Annabi, Saboda Annabi ya karantar dasu kuma yayi a gaban su har ma ya kwadaitar da wannan ibadar.
Yawaita nafila yana kawo abubuwa kamar haka :
*Gidan mutun yana albarka
*Darajar dan Adam tana karuwa
*Yana sanya mutun yazama abokin Manzo sallal lahu alaihi wassalam a gidan aljannah.
*Nafila na zama abokiyar hira ga dan Adam a cikin kabari.
*Zai kara maka son ALLAH
*Tana maida dan Adam yazama mutanen kirki.
*Samun ladar aikin hajji da umrah
*Kankarewar Zunubai.!!
Yan uwa musulmi masu albarka a yadda duniya ta chanza a yanzu dole ne mu rungumi koyar wa Manzo sallal lahu alaihi wassalam da duk abubuwan da ya karantar damu.
ALLAH ka gafarta mana kayi mana rahama kabamu lafiya da zaman lafiya, Ya ubangiji ALLAH kayi rahama garemu ka biya mana bukatun mu ka haskaka rayuwar mu, Ameen
©®Ibrahim Rabilu Tsafe Alzamfari. 07064282182
Jumu’ah 20-Rabi’ul auwal-1439
Friday 15-December-2017 AB
2017-12-15 21:52 (edited 2017-12-15 22:03 by ibnhujjah ) · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 34 user
This Week : 115 user
This Month : 357 user
Total all : 270623 visitors
LAST PAGES