Ring ring

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah FASSARAR KHUDBAR JUMU’AH DAGA MASJID ABI HURAIRA AREA 2 TSAFE JIHAR ZAMFARA

Bayan mukaddimah…..
Yan uwa musulmi masu albarka yau khudbar mu zata yi magana ne game da #MUHIMMANCIN_SALLAR_DARE (kiyamul laili)
Yan uwa musulmi a makon da ya gabata munyi khuduba ne game da sallar nafila..
To yau in sha Allah Zamu yi magana ne game da Sallar Dare wato kiyamul laili.
Hakika Allah ya yabi masu yin sallar dare a cikin suratul sajadah, “ALLAH ya kan rokon sa kuma suna ciyar da abunda muka basu, Suna tashi sallar dare, suna da makoma ta kwarai”
Hakika saboda kaunar mu da Allah yake yi ya bamu damar aikata ibadu kala kala har ma yakan bamu lada idan mun aikata.
Manzo sallal lahu alaihi wassalam yace “Mafificiyar sallah itace sallar nafila bayan ta sai sallar dare”
Hakama Manzo sallal lahu alaihi wassalam yana cewa “Sallar da Allah yafi so itace sallar dare”
Yan uwa musulmi masu albarka lallai wannan sallar wato sallar dare tana karawa ihlasi.
Hakika tsayuwa cikin dare yana karawa bawa tsoron Allah da natsuwa, Hakama duk ranar da dan Adam yayi sallah to zaiji natsuwa da kwanciyar hankali.
Wata rana Manzo sallal lahu alaihi wassalam yace ma sahabin sa “In fada maka wata hanyar alkhairi??
Sai sahabin yace eh, Sai Manzo sallal lahu alaihi wassalam yace ‘Ka yawaita azumin nafila, Da sadaqah domin sadaqah tana cinye zunubai kamar yadda ruwa suke kashe wuta sai kuma ka lizimci sallar dare”
Yan uwa musulmi masu albarka muhimmancin sallar dare baya misaltuwa, Manzo sallal lahu alaihi wassalam yace “ALLAH yayi rahama ga wanda ya tashi yayi sallar dare”
Hakika yan uwa musulmi sallar dare tana cikin salloli masu karawa dan Adam ihklas.
Manzo sallal lahu alaihi wassalam shine baban abun koyi garemu baki daya, Hakika Manzo sallal lahu alaihi wassalam ya kasance yana tsayuwar dare har kafasun sa su fara tsagewa har Aisha radiyyallahu anha tace masa miyasa kana Manzo Allah kake Ibadah kamar haka??
Sai Manzo sallal lahu alaihi wassalam yace Shin bazan zamo bawa mai godiya ba??
Yan uwa musulmi masu albarka hakika yawan yin sallar dare yana kauda bala’oi da musibuh.
Sallar Dare tana gyara halaye kuma tana gyara halaye.
Ibn hajr asqalani yace ‘Ita sallar dare tana wanke zukata’
Saboda muhimmancin sallar dare Manzo sallal lahu alaihi wassalam ya hore mu da yin sallar dare inda yake cewa “NA hore Ku da sallar dare domin tana share zukata”
Hakika sallar dare tana kara lafiya da kwarin jiki,
Ina wadanda basu da lafiya likita yace sai sun rika motsa jiki duk safiya???
To ga exercise daga likitan likitoci Manzo sallal lahu alaihi wassalam idan har ka tsarkake niya to hakika Allah zai baka lafiya da yardar sa.
Ibn Salam ya ruwaito daga cewa Manzo sallal lahu alaihi wassalam yace “Ku yada sallama a tsakanin ku Ku raba Sadakar abinci Ku sada zumunta kuyi sallar dare”
Duk mai kokarin sallar dare Allah zai haska zuciyar sa….
Wata rana Manzo sallal lahu alaihi wassalam yana baiwa sahabbai labari cewa “A cikin aljannah akwai wasu benaye masu tsawo ana ganin abunda ke ciki saboda tsabar hasken su a wata ruwayar har matan da suke ciki ya kwatanta, Sai wani mutanen karkara yace ya Manzo Allah wake da wadannan benayen??
Sai Manzo Allah yace na wadanda suka iya magana ne (Magana mai kyau Sadaka ce) da wanda ya sada zumunci da wanda ya yawaita azumi da wanda ya lizimci sallar dare ”
ALLAH Ya umarci Manzo sallal lahu alaihi wassalam ya tashi yayi sallar dare” KA TASHI KAYI SALLAR DARE KA ROKI UBANGIJIN KA ”
Manzo sallal lahu lahu alaihi yayi addu’a ga wanda ya tada iyalinsa suka yi sallar dare.
Idan mata ta tashi zatayi to tana iya tada mijinta Shima idan bai tashi ba tana iya yayyafa masa ruwa amma idan babu matsala
Yan uwa musulmi masu albarka saboda muhimmancin sallar dare Umar bn Khaddab ya kasance yana tada iyalinsa suyi sallah a karshen dare.
Hakika ALLAH yana sauka a sulisin dare a saman duniyar nan yana cewa “INA MASU NEMAN GAFARA INYI MASU INA MASU NEMAN BIYAN BUKATA IN BIYA MASHI??”
Yan uwa musulmi a yanzu mun bar sallar dare sai a lokachin azumin ramadana.
Idan baka iya tashi da dare to kana iya yin sallar ka bayan isha’i.
Yan uwa musulmi lokachin da yakamata muyi sallar shine misalin karfe 2,3,4 domin shine sulisin dare.
A yanzu muna ganin yadda a duniyance kowa yana neman hanyar rayuwa, Kama daga bidar kudi da sauran su.
Ita lahira babu batun kudi ko wani abu hakika yakamata mu maida hankali dan lahirar mu.
Lallai kada mu kuskura shaidan yayi tasiri garemu.
Mai hankali ne wanda keyi lahirar sa tanadi kafin yaje.
ALLAH Ka taimakemu da taimakon ka ya ubangiji ka yafe mana kurakuren mu.
Ya Allah ka biya mana bukatun mu kayi rahama ga mamatan mu ya amintar damu daga abunda muke tsoro.
(Dan Adam ajizi ne Allah ka gafarta mana abunda muka yi kuskure)
2017-12-31 00:44 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 70 user
This Week : 151 user
This Month : 393 user
Total all : 270659 visitorsUnited States
LAST PAGES