Pair of Vintage Old School Fru

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah HADITHIN ANNABI SHI NE SAMA DA MAZHABAR KO WANE MALAMI:
1. Hadithin Annabi mai tsira da amincin Allah shi ne sama da mazhabar ko wane malami, fiqhunsa kuma shi ne sama da fiqhun ko wane faqihi.
2. Bin mazhabar wani malami daga cikin Malaman Musulunci ba laifi ba ne matukar dai hakan bai kai mutum ga barin yin aiki da wani ingantaccen hadithin manzon Allah mai tsira da amincin Allah ba, in kuma ya kai shi ga barin yin aiki da wani ingantaccen nassin hadithin Annabi to lalle hakan ya haramta a bisa ittifakin dukkan Magabata na kwarai; saboda Annabi Muhammadu ne kawai Allah Ya aiko wa wannan Al'umma, duk kuma wani wanda ba shi ba to mabiyi yake a gare shi, kuma maganarsa shi Annabi tana sama da maganarsa.
3. To amma idan aka sami wata mas'ala da babu nassin Annabi mai tsira da amincin Allah a kanta to a nan dukkan wani malami mai ikon yin ijtihadi sai ya yi ijtihadinsa domin neman kaiwa ga hukuncin Shari'ah a cikinta, duk kuma hukuncin da ya samu kaiwa gare shi cikin ijtihadin nasa to da shi ne zai bauta wa Allah Ubangijinsa.
4. Shi kuma aammiy mara ikon yin ijtihadi irin na Ilmi sai ya yi koyi da wanda zuciyarsa ta fi kwanciya da shi cikin mujtahidan da suka yi ijtihadin Ilmi a cikin wannan mas'ala wacce babu ingantaccen nassin Manzon Allah mai tsira da amincin Allah a cikinta. Wannan shi ne abin da Shari'ar Musuluncin ta tabbatar.
5. Da wannan ne za a san cewa: wajibi ne a kan ko wane musulmi ya gina addininsa a kan sunnar Annabi mai tsira da amincin Allah; saboda duk wanda ya bar yin aiki da ingantaccen hadithin Annabi mai tsira da amincin Allah cikin wata mas'ala daga cikin mas'aloli kuma cikin zabinsa da jin dadinsa a bisa hujjar cewa: mazhabarsa ta saba wa hadithin, ko wata darika tasa ta saba wa hadithin, ko wani tsari na kungiyarsa ya saba wa hadithin, ko wani tsari na duniyarsa ya saba wa hadithin to lalle wannan ya bace ya bar hanyar Muminai, ya bar fikhun Sahabbai da Tabi'ai da Tabi'ut Tabi'in, Wannan shi ne abin da nassoshin Alkur'ani mai girma da Sunnah mai daraja ke tabbatarwa.
Shaikhul Islam Ibnu Taimiyah ya ce cikin Majmuu'ul Fataawaa 24/202:-
))((.
Ma'ana: ))Amma wannan da Sunnah ta bayyana gare shi, sannan ya yi zaton cewa waninta ya fi ta alheri, to shi dan'bidi'ah ne, kai kafiri ne ma((.
Ya kuma ce cikin littafin 27/125:-
))((.
Ma'ana: ))Wanda ya bar nakalin da aka gaskata daga mai fada wanda yake ma'asuu'mi, sannan ya bi nakalin da ba a gaskata ba daga mai fadan da ba ma'asuu'mi ba, hakika ya bace bata mai nisa((.
Allah Ka tausaya wa wannan Al'ummah Ka cusa mata ganin girman Annabi da son bin sunnarsa a cikin zukatanta. Ameen.
2018-03-29 06:23 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 11 user
This Week : 34 user
This Month : 21 user
Total all : 270287 visitors
LAST PAGES