Pair of Vintage Old School Fru

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah HAKURI BAYA BACI

Gaskiya ne rayuwa makaranta ce, Amma wanda zai fi cin jarrabawar wannan makarabta shine mai hakuri da hankalta don kiyaye gaba.Pls ka matashiya game da rayuwa da fatan Allah ya kara mana hakuri da Junan mu, amin
1. Wanda ya ganka a cikin matsala ko bukata a rayuwar ka, ya tsaya ya taimaka maka har aka dace ka fita daga wannan damuwa hakika masoyin ka ne, Don haka abin so shine kayi ta masa addu’a da fatan samun damar ka saka masa, amma ka kiyaye kada kayi masa Butulci, Kuma kayi hakuri dashi kada ka kosa da shi in ya bukaci agajin ka.
2. Wanda ya ganka a cikin matsala ya rabu da kai, wato ya fita sha’anin ka, yaki tausaya maka ko agaza maka. Shi wannan in ka samu dama ka yi kokarin koya masa darassi mai kyau wajen yi masa alheri, kada kayi watsi dashi in yazo nema gun ka, hasali ma abin so shine ka yafe masa abinda yayi maka, insha Allahu hakan zai zamo darassi gareshi a rayuwa ya gane yin hakan ba dai-dai bane ya gyara a gaba.
3. Wanda ya yi ta kai kawo don ganin ka shiga matsala da damuwa a rayuwar ka, ko yayi ta nuna maka kiyayya da kulle-Killen sharri don dai ayi maka wulakanci, ko ya jawo aka musguna maka.. Allah sarki shi wannan ka bar shi da Allah zai saka maka, ka daure ku jure har ka samu mafita, daga nan ka yi fatan kada ya sake samun damar cutar da kai. Amma shima kayi hakuri ka yafe masa ka dogara ga Allah da ya baka dacewa ka Tsira daga sharrin sa.
4. Wanda ka yiwa alheri wato ka taimake shi a rayuwar sa, ka tsaya akan hidimar sa, Amma ya dawo yana rama maka da zagi, ko yana aibata ka, ko ya nuna maka rashin godiya. To ka da ka damu, kayi hakuri ka zuba masa ido, kuma kada kayi masa gori, hakika mafi yawan masu butulci rayuwar su cikin nadama take karewa. Kuma tabbas zai samu wanda zai yi masa fiye da abinda yayi maka. Kia kuma Allah zai saka maka.
‘Yan uwa mu sani duk abinda kowa ya shuka shi zai girba a duniya da lahira. Nakan ji tsoro in na tuna cewa: Wanda ya aikata alheri ko da baifi kwayar zarra ba zai gani, Haka nan wanda ya aikata sharri shima ko da bai fi kwayar zarra ba zai gamu da sakamakon abin da yayi a duniya da lahira.
Masu magana kance alhaki kui-kuyo ne mai Shi yake bi..
Allah ya tsare mana imanin mu da mutumcin mu, amin
Daga Malam Aliyu Said Gamawa:
2017-12-17 05:32 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 74 user
This Week : 155 user
This Month : 397 user
Total all : 270663 visitorsUnited States
LAST PAGES