Old school Swatch Watches

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah HANYOYI GUDA 24 DA SUKE SANYAWA ALLAH YA AMSA ADDU'AR BAWA

Darasi na farko-(1)


1-Hanya ta farko

*"Tsarkake niyya da Ikhlasy lokacin rokon Allah da dukkan ibada baki daya"*

Duk lokacin da bawa zai roki Allah,to babban abinda ya kamata ya gabatar shine Ikhlasy,wato kada ya roki kowa sai Allah shi kadai,domin addua ibadace kuma Addua itace mafi girman aikin dha'a,kuma itace mafi hanyar da bawa yake samun kusanci zuwa ga Allah,kuma Allah baya amsar dukkan wani aiki sai wanda akayi da ikhlasy da kyakkyawar niyya,wato anyi aikin dan Allah shi kadai,da kuma wanda akayi dan neman yardar fuskar Allah mai karamci.

Allah yana cewa:
(ﻭَﺃَﻥَّ ﭐﻟْﻤَﺴَـٰﺠِﺪَ ﻟِﻠَّﻪِ ﻓَﻼَ ﺗَﺪْﻋُﻮﺍْ ﻣَﻊَ ﭐﻟﻠَّﻪِ ﺃَﺣَﺪﺍً )ﺍﻟﺠﻦ 18:
(Kuma lalle ne wurãren sujada na Allah ne,saboda haka kada ku kira kõwa tãre da Allah "da su, a cikinsu").

Kuma Allah yana fada:
(ﻓَﭑﺩْﻋُﻮﺍْ ﭐﻟﻠَّﻪَ ﻣُﺨْﻠِﺼِﻴﻦَ ﻟَﻪُ ﭐﻟﺪّﻳﻦَ ﻭَﻟَﻮْ ﻛَﺮِﻩَ ﭐﻟْﻜَـٰﻔِﺮُﻭﻥَ)ﻏﺎﻓﺮ : 14

(Sabõda haka ku kirãyi Allah,kunã mãsu tsarkake addini a gare Shi,kuma kõ dã kãfirai sun ƙi).

Daga Ibn Abas ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﻤﺎ daga Manzon Allah,ya ce da shi:
*(Idan zakayi roko,to ka roqi Allah shi kadai,kuma idan zaka nemi taimako to kanemi taimakon Allah shi kadai.......)*
@ﺭﻭﺍﻩ ﺃﺣﻤﺪ ‏( 1/293، 307 ‏)،ﻭﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ‏( 2511 ‏) ، ﻭﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ‏( 7957 ‏)

2-Hanya ta Biyu-2

*"Kayi hakuri da juriya wajan rokon Allah da naci da yawan nanatawa wajan rokonsa,kada kayi gaggawa acikin rokon Allah"*

Yana cikin babban ladabin bawa ga Allah lokacin addua da rokonsa,bawa ya nace yayi ta rokom Allah babu gajiyawa tare da nanatawa da kwadayin lallai Allah yana amsa adduar wanda ya nace.

Daga Abi Hurairata ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ yana cewa:
Manzon Allah s.a.w yana cewa:
*(Allah yana amsa adduar dayanku matuqar bai gajiyaba,bai ce ba,naroki Allah na rokeshi amma bai amsamin ba)*
@ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ﻓﻲ ﺍﻟﺪﻋﻮﺍﺕ ‏( 6340 ‏)،ﻭﻣﺴﻠﻢ ﻓﻲ ﺍﻟﺬﻛﺮ ﻭﺍﻟﺪﻋﺎﺀ ‏( 2735 ‏)

Kuma an ruwaito Daga Abi Hurairata ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ yana cewa:
Manzon Allah s.a.w yana cewa:
*(Allah bazai gushe ba yana amsa adduar dayanku ba,matuqar bai roqi sabon Allah ba,ko yanke zuminci,mutuqar baiyi gaggawaba)* sai suka tambayesa minene gaggawa a addua?? Sai yace:
*(Shine mutum yace ni nayi roqon nayi roqon amma ba'a amsamin ba,sai ya gaji ya daina adduar)*
@ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ ﻓﻲ ﺍﻟﺬﻛﺮ ﻭﺍﻟﺪﻋﺎﺀ( 2735 ‏) .

ﺍﺑﻦ ﺍﻟﻘﻴﻢ رحمه الله:
Yana cewa:
*"Yana daga cikin dalilan da yake sanyawa Allah yaqi amsa adduar bawansa,bawa yariqa gaggawa acikin addursa,yaroqi Allah sai kuma yariqa gaggauwar son ganin biyan buqata daga nan sai ya gajiya yace naroqa naroqa ba'a amsamin ba sai ya daina adduar........."*
@ﺍﻟﺠﻮﺍﺏ ﺍﻟﻜﺎﻓﻲ‏(ﺹ 10‏).

3-Hanya ta Ukku

*"Tuba da komawa zuwa ga Allah daga dukkan zunubai da laifiuka"*

Mafi yawan masu koken Allah baya amsa adduarsu,zaka samesu masu yawan zunubaine da sabon Allah,kuma basu tuba da kowa zuwa ga Allah.

Daga Umar Bn Khaddab ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ‏ yana cewa:
*"Ka kame daga dukkan abinda Allah ya haramta maka nq zunubai da laifuka sai Allah ya riqa amsa adduarka..."*

Wani daga cikin magabata na kwarai yana cewa:
"Dukkan wanda yake dauwama acikin sabon Allah,baya tuba,to kada yayi tsammanin Allah zai riqa amsa adduarsa"

4-Hanya ta Hudu

*"Kokarin cikin halal da amfani da rayuwa da dukiyaar halal da nisantar cin haramun"*

Hakika dukkan wanda ya yawaita amfani da dukiyar haramun,to yana toshe kokafin amsa adduarsa ne a wajan Allah.

Manzon Allah s.a.w yana cewa:
*(ﺃﻳﻬﺎ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺇﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻃﻴﺐ ﻻ ﻳﻘﺒﻞ ﺍﻻ ﻃﻴﺒﺎ ﻭﺍﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻣﺮ ﺍﻟﻤﺆﻣﻨﻴﻦ ﺑﻤﺎ ﺃﻣﺮ ﺑﻪ ﺍﻟﻤﺮﺳﻠﻴﻦ ، ﻓﻘﺎﻝ : ‏( ﻳﺎ ﺃﻳﻬﺎ ﺍﻟﺮﺳﻞ ﻛﻠﻮﺍ ﻣﻦ ﺍﻟﻄﻴﺒﺎﺕ ﻭﺍﻋﻤﻠﻮﺍ ﺻﺎﻟﺤﺎ ﺍﻧﻲ ﺑﻤﺎ ﺗﻌﻤﻠﻮﻥ ﻋﻠﻴﻢ (( ﺍﻟﻤﺆﻣﻨﻮﻥ : 51 ﻭﻗﺎﻝ : ‏( ﻳﺎ ﺃﻳﻬﺎ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﺃﻣﻨﻮﺍ ﻛﻠﻮﺍ ﻣﻦ ﻃﻴﺒﺎﺕ ﻣﺎ ﺭﺯﻗﻨﺎﻛﻢ (( ﺍﻟﺒﻘﺮﺓ : 172)*
Sannan Manzon Allah s.a.w ya ambaci wani mutum,wanda yayi tafiya mai nisa mai gizo mai kura har gashin kansa ya nannade,sai ya daga Hannunsa zuwa sama yana cewa;
"YA RABBI YA RABBI" amma abincinsa haramunne,kuma abin shansa haramunne,ya yi rayuwa cikin haramun,sai Manzon Allah s.a.w yace:
*(Ta yaya Allah zai amsa adduarsa??*)*.
@ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ ﻭﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ

ﺳﻌﺪ ﺑﻦ ﺃﺑﻲ ﻭﻗﺎﺹ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ
Ya kasance cikin wadanda Allah yake amsa adduarsu kai tsaye babu bata lokaci,
Yana cewa:
*"Bana sanya wata loma acikin bakina face nasan daga ina take kuma ina tafito..."*

Malamai sunce wannan shine babban sirrin amsa adduarsa akowane lokaci.

5-Hanya ta biyar

*"Kyautata zato ga Allah madaukakin sarki,domin Allah yana amsa adduar wadanda suke kyautata zato akansa ne"*

Manzon Allah s.a.w yana cewa:
*(Kuriqa rokon Allah kuma masu kyautata zato da sa ran Allah yana amsa addu'o'inku,domin Allah baya amsa addua daga zuciyar datake rabbakana daga Allah mai wasa da rashin kyautata zaton Ana amsa mata)*
@ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ‏( 3479 ‏) ﻭﺣﺴﻨﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺢ

Awani Hadisin yana cewa:
*(Ina inda bawana yake zatona,kuma ina tare da shi duk lokacin da ya ambaceni,.......)*
@ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ‏( 7405 ‏) ، ﻭﻣﺴﻠﻢ ‏( 2675 ‏) ،

Allah ne mafi sani.

Allah ka sanya mu cikin bayinka da kake amsa addursu.
2018-06-22 23:41 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 23 user
This Week : 46 user
This Month : 69 user
Total all : 270252 visitorsUnited States
LAST PAGES