Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah HANYOYIN SAMUN INGANTACCIYAR HADDAR
ALQUR'ANI:
1. Ka fara haddar ka da addu'ar neman taimakon
Allah cikin wannan niyya taka ta alheri.
2 Ka kula sosai da kanka wajen nisantar
kazamtar haramun, wato ka tsaya wajen cin
halal, domin cin
haram yana toshe basirar Dan Adam
3. Ka nisanci fara hadda don burin samun dukiya,
kuma ka cire kwadayin abin duniya a zuciyarka.
Haddar Alqur'ani bata zama a cikin kwakwalwar
duk wanda ya
matsu yaga ya tara dukiya a cikin haddar sa da
zafi-zafi.
4. Kayi karatu a wajen Malami na Allah wanda
yasan Karatun, Kuma serious malami wanda ya
maida hankalinsa akan hidimtawa Alkur'anin.
5. Ka nemi goyon bayan mahaifan ka tare da
rokon addu'arsu, don sanya albarka daga
iyayenka ginshiki ne wajen nasarar samun haddar
ka cikin sauki.
6. Kaifin basira da hazaqa yana taimakawa wajen
saurin samun yin hadda mai kwari cikin karamin
lokaci
7. Ka fara hadda da niyya mai kyau, wato ka
zamo mai kwadayin son karatun da burin haddar
alkur'ani.
8. Ka zamo mai juriya akan kowacce irin wahalar
da zaka riska a wajen neman karatun ka, ka cire
son hutu da yawan kasala ko son nishadi da
wargi da zai jawo maka lalaci.
9. Tanadin abinci yana da muhimmanci don ka
samu natsuwa, don ba'a iya hadda mai kyau da
yunwa amma kar kace sai kaci mai kyau kasha
mai kyau a kullum.
10. Kar ka sanya gaggawa wai sai ka gama
hadda a karamin lokaci, ka natsu ka bi a hankali
domin
ba'a samun ilimi a cikin dare daya.
11. Samun abokan karatu na kirki da zaku na
tafiya tare cikin hadda yana taimakawa, amma ka
kiyaye Idan fa abokanka suka zamo na banza, ko
wadanda basa son karatun ko masu kasala to
tabbas ka hadu da matsala da ci baya a harkar
karatun ka.
12. Ka tsara gwargwadon abinda zaka na
haddacewa a kullum, wato kamar ka tsara cewa a
duk cikin kwana 3 zaka yi haddar allonka ko shafi
daya ko biyu ko makamancin haka..
13. Ka rika karanta wuraren da ka haddace a
cikin Sallar ka ta farilla da nafiloli a kowanne
wuni.
14. Idan da dama ka nemi allo ka rubuta da
kanka wajen da kake son ka haddace, ko ka
samu littafi mai rubutun da idon ka zai karanata
sosai, sannan kayi ta QwamI.. Ba-ji ba-gani.
15. Ka tsarawa kanka lokaci a cikin safiya da
maraice kana tilawa na maimaita wurin karatun
ka adadi mai yawa, wato kana biyawa a kullum
kamar sau 100 in zaka iya.
16. Ka za6i yin tilawa da dare da jijjifin safiya, ka
tsara yadda zaka Qaranta barcinka, kuma abinda
yafi shine kana bacci da wuri don ka samu tashi
cikin dare, ka kula wajen cin abinci madaidaici,
Ka takaita yawo da surutu maras amfani da
zaman wurin hira. kuma ka rage yawan abokai
17. Ka kula sosai da yawan ibada da nisantar
aiyukan sa6o.
18. Ka gujewa sauraron wakokin banza da
raye-raye da kallon film don suna makantar da
zuciya.
19. Ka tsare harshen ka daga batsa da zagin
mutane da kallon haramun da latse-latsen waya
maras amfani.
20. In kana samun wahalar rike hadda kayi hakuri
ka dogara ga Allah, ka yi juriya ka nisanci debe
tsammani da karaya a zuciyar ka. Lallai in kana
himma da dagewa zaka samu taimakon Allah.
Ina rokon Allah ya karfafa niyyar mu, ya cika
mana burin mu ya hore mana saukin hadda ya
bamu karatu mai albarka, amin
2018-06-12 13:19 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 12 user
This Week : 35 user
This Month : 22 user
Total all : 270288 visitorsUnited States
LAST PAGES

Insane