XtGem Forum catalog

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah *HUKUNCE-HUKUNCEN MAI TAKABA*
*Tambaya:*
Assalamu alaikum wa rahmatullaah. gafarta Malam pls ayi mana bayani koda a takaice ne dangane da hukunce - hukuncen takaba... Na shiga wajen mahaifiya dazu, take cewa in tambaya mata Malamai tanadin shari'a akan wannan al'amari. Nagode
*Amsa:*
Wa alaikum assalam.To dan'uwa ina rokon Allah ya jikan mahafinku, akwai hukunce-hukunceda suka shafi takaba, ga muhimmai daga ciki:
*1.* Mai takaba za ta zauna a gidan mijinta ba za ta fita ba, har sai ta gama iddarta, wacce take wata hudu da kwana goma, kamar yadda aya ta: 234 a suratul Bakara take nuni zuwa hakan .
*2.* Ba za ta saka kaya masu kyau ba, don haka za ta guji ado, kamar yadda hadisin Abu-dawud mai lamba ta: 2304, ya yi bayanin hakan.
*3.* Shari'a ta hana mai takaba ta sanya turare, kamar yadda hadisin Bukhari mai lamba ta: 5343, ya tabbatar da hakan,
*4.* Malamai suna cewa mai takaba ba za ta sanya tozali ba , kamar yadda hadisin Nasa'i mai lamba ta: 3565 ya bayyana hakan.
*5.* An hana mai takaba yin lalle, kamar yadda hanin ya zo a hadisin Abu-dawud mai lamba ta: 2304.
*6.* Idan wata bukata ta kama za ta iya fita daga gida, ko da rana ne ko da dare.
*7.* Za ta iya yin Magana da mazan da ba muharramanta ba, idan bukatar hakan ta kama, saidai ta guji, sanyaya murya, kamar yadda aya ta 32 a suratul-ahzab ta hana sanyaya murya ga wadanda ba muharramai ba.
*8.* Babu wani launi na kaya na musamman da aka shar'anta mata ta sanya, don haka, duk kayan da ba kwalliya a jikinsu ya halatta ta sanya su .
*9.* Za ta iya yin wanka da sabulun da yake ba mai kanshi ba .
*10.* Za ta iya zama ta yi hira da makusantanta, har ma za ta iya bude gashin kanta, idan su duka muharramanta ne .
*11.* Bai halatta wani ya nemi auranta ba, har sai ta gama idda, saidai za'a iya yin jirwaye mai kama da wanka, kamar yadda aya ta 235 ta yi nuni zuwa hakan.
*12.* Idan mai takaba tana da ciki, to iddarta ita ce: haife abin da take dauke da shi, kamar yadda hadisin Subai'a mai lamba ta: 5014 a Sahihul Bukhari ya tabbatar da hakan.
Allah ne mafi sani.
*Amsawa*
*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*
2018-07-02 20:49 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 81 user
This Week : 162 user
This Month : 404 user
Total all : 270670 visitors
LAST PAGES