Polly po-cket

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah HUKUNCIN CIN ABINCIN CHRISTMAS

Takaitaccen bayani akan cin abincin christmas.
1. Komitin Fatawa na
Saudiyya karkashin Ash Shaikh Abdul’Azeez bin Abdallah ibn Baz RahimahUllah sun fada a cikin “Fatawa
Islamiyyah” Cewa:
“Baya halatta ga musulmi yayi
alaqa da kafurai
a lokacin hutunsu da
bukukuwansu. Bai halatta
yayi murna ga wadannan
bukukuwan ba, ko kuma yaki fita
aiki sabo da
bikin.
Kuma hukuncin daya ne, ko dai
hutu ne
na wani bikin addini, ko kuma wani
bikin
kafurci.
Domin yin haka koyi ne da
makiya Allah
wanda Haramun ne.
Komitin Sun kafa hujja
da Hadith
wanda Annabi(SAW) yace:
“”
” Duk Wanda Yayi kamanceceniya (koyi) da wasu mutane, to shima yana cikin su ”
(Fatawa Islamiyya Volume 1/255-256).
Sabo da haka, ba
yanda za’ayi
ka karbi kyautan Christmas kuma ka
fadawa
mutane cewa “baka murna/
celebration ga
bikin”.
2. Wata rana Umar R. A. Yana tafiya da dansa Abdullahi R. A. Sai wani Christian (kirista) Ya bawa Abdullahi mangoro (fruit), Sai Umar R. A. Yace wannan fa? Sai Christian yace na bashi ne saboda murnar Christmas, Sai Umar Ya fadawa Abdullahi cewa Ya jefar da mangoron.
3. Amma naji wani yana cewa a karbi abincin Christmas aci. Kuma yace ko da sunan jesus ne suka yanka a karba aci.
Wannan maganar ta sabawa ayar Al-Qur’ani mai girma:
Allah Ta’ala yace baya halatta ga musulmi
yaci yankan
da ba’a ambaci sunan Allah ba.
Allah(SWT) yace:
“Saboda haka kuci daga abinda aka
ambaci
sunan Allah a kansa, idan kun
kasance masu
imani da ayoyinSa”( ka dubi suratul An’am Q6/ 118).
“Kuma mene ne ya same ku, baza ku
ci ba
daga abinda aka ambaci sunan
Allah a
kansa ba, alhali kuwa, hakika, Ya rarrabe
muku
daki-daki, abinda Ya haramta a
kanku, face fa
abinda aka bukatar da ku bisa lalura
zuwa
gare shi? Kuma lalle ne masu yawa
suna
batarwa, da son zuciyoyinsu, ba da
wani ilmi
ba. Lalle ne Ubangijinka shine Mafi
sani ga
masu ta’addi”(Surah ta Q6/ 119).
“kuma kada kuci daga abinda ba’a
ambaci
sunan Allah ba a kansa. Kuma lalle
ne
shi, fasikanci ne. Kuma lalle ne
shaidanu, hakika
suna yin ishara zuwa ga
masoyansu, domin
suyi jayayya da ku. Kuma idan kuka
yi musu
da’a, lalle ne ku, hakika, masu shirki
ne”(Qur’an 6:121).
WADANNAN AYOYI SUN NUNA DUK WANDA YACE KACI ABINDA BA’A YANKA DA SUNAN ALLAH BA FASIQI NE KUMA SHAIDAN NE SHI.
Har yanzu ka dubi Fatawa
Islamiyya. Asalin Ahl
al-kitab da aka halatta cin yankansu
ma, akwai
sharadin sai sun ambaci sunan Allah
a kansa, idan kuma basu ambaci
sunan Allah a
kansa ba, to haramun ne a ci, domin
hakan
fasikanci ne. Sun kafa hujja da ayan
da muka
rubuta a sama Q6:121.(Fatawa
Islamiyya Volume 6/317-318).
4. Kuma ya kamata mutane su lura, su gane su waye ne asalin Ahl-Al-Kitaab.
An samu wasu Christians a
lokacin Sayyidina Umar (R.A.) da Sayyidina Aliy (R.A.), sai aka tambaye su cewa shin Ya halatta muci yankan su, sai suka ce:
“kada
kuci yankansu kuma kada ku
auresu, domin
babu abinda suka gada daga
Addinin
Yahudawa da Nasara sai dai Zina da
Shan
gida” (Ka dubi ADWA’UL BAYAN na Sheikh Muhammad Al-Amin Ash-Shankidi 10/74).
5. KUMA BAI HALATTA KACE HAPPY CHRISTMAS GA WANI BA.
Allah Ta’ala muke roko Ya dora mu akan daidai.
2017-12-24 23:44 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 36 user
This Week : 117 user
This Month : 359 user
Total all : 270625 visitors
LAST PAGES