Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah HUKUNCIN SAKIN MAI HAILA Tambaya: Malam mun samu rikici da matata ko ya halatta na sake tana haila?? Amsa: Ya haramta a saki mace lokacin da take haila, saboda fadin Allah "Ya kai Annabi idan za ku saki mata, to ku sake su a farkon iddarsu) Suratu Addalak aya ta farko, wato a farkon tsarkin da ba ku take su a cikinsa ba. Ana nufin a halin da za su fuskanci idda sananniya, wannan kuwa ba ya faruwa sai idan ya sake ta tana da ciki ko tana cikin... tsarkin da bai take ta ba, domin idan ya sake ta a cikin haila to ba ta fuskanci idda ba, saboda hailar da ya sake ta a ciki ba za’a kirga da ita ba, haka kuma idan ya sake ta tana da tsarki bayan ya sadu da ita, domin bai sani ba shin ta dauki ciki ta yadda iddarta za ta zama irin ta mai ciki ko kuma ba ta dauka ba ta yadda za ta yi idda da haila, saboda rashin tabbacin haka sai sakin ya haramta. Ya tabbata a cikin Bukhari da Muslim cewa : Ibn umar ya saki matarsa tana haila, sai Umar ya bawa Annabi s.a.w. labari, sai Annabi s.a.w. ya yi fushi, sai ya ce "ka umarce shi ya mayar da ita sannan ya rike ta har ta yi tsarki sannan ta yi haila, sannan ta yi tsarki, sannan in ya so ya rike ta ko kuma ya sake ta kafin ya sadu da ita, wannan ita ce iddar da Allah ya umarta a saki mata a ita" ANA TOGACE GURARE GUDA HUDU WADANDA SAKIN MACE MAI HAILA YAKE HALLATA : A. idan sakin ya kasance kafin ya kadaita da ita ko kafin ya sadu da ita, to anan ya halatta ya sake ta tana haila, saboda anan bata da idda, sakinta ba zai zama ya sabawa fadin Allah madaukaki (Ku sake su a farkon iddarsu) ba B. idan ta yi hailar ne tana da ciki kamar yadda aka riga aka yi bayani a baya. C. idan ya sake ta ne bayan ta fanshi kanta, (KUL'I) to anan babu laifi ya sake ta tana haila. D. Idan ya yiwa matarsa I'laa'i kuma aka yi watanni hudu bai dawo ba. Allah ne mafi sani Jamilu Yusuf Zarewa
2018-02-25 21:44 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 29 user
This Week : 85 user
This Month : 173 user
Total all : 270439 visitors
LAST PAGES

XtGem Forum catalog