Pair of Vintage Old School Fru

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah HUKUNCIN SAUKEWA MAMACI ALQUR'ANI BAYAN YA MUTU ?? Tambaya : Wai Malam Meye Hukuncin Saukewa Mamaci Al-qur'ani ? Amsa: To malamai sun yi sabani akan wannan mas'ala zuwa maganganu guda uku : 1. Bai halatta ba, saboda ba'a samu wani nassi da yake nuni zuwa haka ba, kuma ita ibada ba'a yinta sai da nassi na musamman, sannan kuma mutum ba shi da wani abu sai aikinsa, kamar yadda aya ta 39 da take cikin suratu Najm, take nuni zuwa haka, tun da ba'a samu ba, yin hakan zai zama bidi'a, wannan ita ce maganar farko ta Shafi'i. 2. Ya halatta ayi, saboda hadisan da suke nuna cewa mamacin yana iya amfana da abin da mai rai zai masa, kamar hadisan da suka yi umarni da yi masa sallah da nema masa gafara bayan ya mutu, da yi masa sadaka, wannan shi ne maganar mafi yawan malamai, har wasu marubuta ma sun hakaito ijma'i akan haka, saboda mutane sun jima suna yi kuma malamai ba su yi musu inkari ba. 3. Akwai wadanda suka tafi akan cewa : idan dansa na cikinsa ya yi masa, to ladan zai same shi, amma wanda ba dansa ba, ba zai yi masa ba, saboda fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi" Dan mutum yana daga cikin aikinsa" Abudawud ya rawaito shi kuma albani ya inganta shi a sahihu sunani-abi-dawud hadisi mai lamba ta : 2528 . Wasu malaman, suna rinjayar da magana ta uku, saboda fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi : "Idan dan'adam ya rasu ayyukansa sukan yanke sai dayan abubuwa guda uku : sadaka mai gudana, ko ilimin da ake amfana da shi, ko da nagari da yake masa addu'a" kamar yadda Tirmizi ya rawaito shi kuma ya inganta shi a hadisi mai lamba ta :1376. Wadancan hadisan kuwa da masu Magana ta biyu suka kafa hujja da su, to za'a yi amfani da su ne a iya inda suka zo, amma ba za'a yi kiyasin karatun qur'ani akan su ba . Don neman Karin bayani : duba majmu'ul fataawa :246 da Nailul Audaar 42 da Ahakamul jana'iz shafi na : 171. Allah ne ma fi sani.
Dr Jamilu Yusuf Zarewa
2018-01-18 10:59 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 18 user
This Week : 574 user
This Month : 816 user
Total all : 271082 visitors
LAST PAGES