Duck hunt

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah Tambaya:“Malam menene hukuncin mai yi wa kishiyarta asiri tana bunnewa, kuma ta shiga tsakanin ‘ya’yanta da mahaifinsu, duk ta hanyar asiri”?
.
Amsa:Yi wa wani asiri ta hanyar raba shi da wani da yake kauna da juyar da shi daga halin kauna da soyayya zuwa halin gaba da kiyayya, mummunan aiki ne, kuma nau’i ne na sihiri da ake kira ‘Sihrut Tafrik’, ko ‘As-Sarf’, wato sihirin rabawa tsakanin ma’aura, ko masoya, ko juya hankalin wani da susuta shi da zautar masa da hankalinsa daga wani abu da zai amfane shi zuwa mai cutar da shi, ko kuma daga kaunar abin kaunarsa ko iyayensa zuwa kyamars u da bijire musu. Akwai hanyoyi da dama da masu irin wannan mugun aiki su kan bi wurin cimma burinsu. Hukuncinsa a musulunci ya zo kurukuru a cikin al-Qur’ani mai girma inda Allah Madaukaki ya ambaci cewa kafirci ne, kuma malamai sun bayyana cewa duk wanda aka kama shi da irin wannan aiki to hukuncinsa shi ne alkali ya sa a kashe shi kisan kafirci da ridda ta barin addinin musulunci. Don haka ya wajaba wannan mata da duk wani mai mummunan aiki irin nata mai irin wannan bamagujiyar mugunta da bakar aniya, ya ji tsoron Allah ya tuba.
Lalata kishiya ta hanyar sihiri da raba ta da mijinta da shiga tsakaninta da ‘ya’yanta ba shi ne zai jawowa mai neman a yi mata sihirin alherin duniyar da take fada da kishiyar a kansa ya dawo gare ta ba. Arzikin duniya da na lahira duk a gun Allah yake, kuma babu wata hanya da za’a same shi sai da yardarsa. Yaya za a yi kuwa a ce mutum mumini ya jefa dan uwansa cikin damuwa, ya hana masa kwanciyar hankali; saboda kawai yana ganin cewa shi ne ya hana shi samun wani abin duniya ko kadaituwa da kaunar miji da soyayyarsa, kuma musamman ma a ce ta hanyar kafircewa da Allah da bautawa aljanu. Gaskiya wannan ba karamar tabewa ba ce, da kekasar zuciya, da rashin tsoron Allah, da fito-na-fito da kaddararsa, da rashin yarda da lamarinsa da dogaro da shi.
Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam fa ya gaya mana cewa duk wanda ya je wurin boka ko dan duba, kuma ya tambaye shi kan wani abu har ya gaskata shi, to ya kafirta da abin da aka saukarwa (Annabi) Muhammad sallalllahu alaihi wa sallam.
A wata riwayar kuma ba za’a karbi sallarsa ta kwana arba’in ba. Wannan wanda ya gaskata kenan, ba tare da ya aikata sihirin ba. Kuma mafi rinjayen maganar malamai ita ce wannan tambayar da gaskatawar kafirci ne amma karami, ba mai fidda mutum daga musulunci ba. Amma mai aikata sihirin da mai ba da kudi da umurni a yi wa wani, kuma wanda ake ba wa umurnin ya cika sharuddan da aljanun ke nema a yi musu, to duk wannan aikinsu daya ne da shi bokan, kafircinsu na fita daga addini ne.
Babban abin da ke cikin wannan ma shi ne bautawa shaidanu da aljanu da yi musu da’a cikin abin da suke so, na yanke-yanke ko neman cika wasu sharudda masu dan karen wahala, da bada umurnin a je wani wuri a yi tono a binne. Wannan duk bautawa aljanu ne, bayan dumbin dukiyar da mutum zai halakar ta wannan mummunar hanya. Allah ya tsaremu.
Nasihata ga duk wanda Allah ya jarraba da wannan mummunar ta’ada ita ce ya gaggauta tuba zuwa ga Allah, kuma ya yi watsi da wannan shirka, kuma ya dogara da Allah bisa duk abin da yake nema, sannan ya ji tsoron cewa shi ramin mugunta in an tona shi ba a fa san wanda zai fara fadawa ba.
Daga cikin manyan hadurran da wannan mummunan aiki ya kunsa akwai:
1. Shirka da Allah da bauta wa aljanu. Kila wata ta ce ai ita wurin ‘malami’ kawai ta je ba gun aljan ba, to ya kamata ki gane cewa shi wannan da kike kira malami ba ya iya komai da kashin kansa sai ya yi da’a ga aljanu su kuma su ba shi umurni ya cika musu. Wannan da’ar da kuma cika sharuddan yadda aljanin ya nema shi ne bakar shirka, domin bautawa wanin Allah ne da neman yardarsa, wato sanya masa kishiya ta hanyar mika wani hakkin ibada zuwa ga waninSa, kamar yanka dabba domin waninSa ko da da sunan Allah ne, ko kuma cika wasu sharuddan da ba Allah ne Ya ce a cika su ba, musamman kuma wurin bautawa wanda za a yi wannan abu dominsa. Allah kuwa ya yi kashedi ga dukkan al’umma cewa “Duk wanda ya yi tarayya da Allah to lallai Allah ya haramta masa shiga Aljanna, kuma makomarsa ita ce Wuta, kuma azzalumai ba su da mataimaka”.
2. Nisantar Allah. Duk wanda Allah ya jarraba da wannan kazamar ta’ada ya fi kowa nisa da ubangiji Mahalicci. Za ka same shi ba ya karatun Al-Kur’ani, ba ya zikirin Allah Ta’ala. Babu abin da yake ba shi sha’awa sai aikin da zai sa shadanin aljaninsa ya yarda da shi.
3. Rashin dogaro ga Allah. Mai sihiri ko kuma mai neman a yi masa sihirin bai yarda da cewa Allah ne abin dogaronsa ba, kuma shi ne mai taimakonsa ba, kuma shi kadai ne mai iya fitar da shi daga kowace matsala, ya kuma dauke masa kowa ce irin damuwa a zuciyarsa ko jikinsa ko abokin zamansa ko zuriyyarsa. Allah Madaukaki yana cewa: “Duk wanda ya dogara ga Allah to Allah ya isar masa”.
2018-02-23 17:03 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 13 user
This Week : 69 user
This Month : 157 user
Total all : 270423 visitors
LAST PAGES