XtGem Forum catalog

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah KADDARA TA RIGA FATA 001
_Shimfida_
i. Farkon Jinyar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Bayan da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya kammala aikin hajjinsa da ya yi a shekara ta Goma bayan hijira wanda a cikinsa ya ce ma Musulmi “Ku yi koyi da aikin hajjina domin ban sani ba watakila ba zan sake haduwa da ku bayan wannan shekarar ba” sai masu zurfin ilmi daga cikin Sahabbai suka fara ji a jikinsu cewa fa lokacin ciratar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama daga wannan duniyar ya kusanto.
Ga shi kuma ana cikin aikin hajjin sai ayar Alqur’ani ta sauka tana ba da labarin cewa, addini kam ya cika, kuma duk wata ni’imar da Madaukakin Sarki yake son yi wa bayinsa ta fuskar dora su a kan shiriya to an kammala ta. Sai suka fahimci cewa, aikin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya zo yi na isar da manzanci ya kare kenan, don haka ajalinsa ya kusa.
Komawar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama Madina ke da wuya kuwa sai ya kwanta
ciyon ajali wanda ya dauke shi tsawon watanni uku, amma dai bai tsananta ba sai a cikin watan Rabi’ul Awwal, wata na uku ke nan bayan aikin hajji.
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya gamu da zafin ciwo fiye da yadda za a kamanta don ko har sai da aka tambaye shi ya ce, mu Annabawa muna da lada biyu ne, don haka a ciwo ma Allah cikin adalcinsa yake ribinya mana nauyinsa.
Mai jinyarsa Uwar Muminai A’ishah ta ba da labarin yadda jikinsa ya gashe, har a kan dauko ruwa mai sanyi a ajiye a gabansa yana sanya hannunsa a ciki don ya dan ji sanyi, amma kuma nan take sai ruwan ya sauya yanayi saboda zafin masassara daga hannayensa masu tsarki.
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya rinka fadin cewa, tabbas mutuwa kina da zafi. Ya Allah ka taimake ni a kan zafin mutuwa!
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya suma a cikin wannan lokaci har sau uku, a ko wanne ya kan tambaya idan ya farka, “Shin ko mutane sun yi Sallah?” akan ce masa, suna nan dai suna jiranka ya Manzon Allah! Sannan ya yi wanka da nufin ya fita zuwa Masallaci. Sai bayan da haka ta faru har sau uku ne, ya hakikance gajiyawarsa a kan fitowa, sannan ya yi umurni a gaya ma Abubakar ya ba mutane Sallah.
_Madogara_
* Duba Sahihul Bukhari a littafin yaqe – yaqe, Babin Mutuwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama.
_Mu hadu a rubutu na gaba…………_
2018-06-19 00:20 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 14 user
This Week : 70 user
This Month : 57 user
Total all : 270323 visitorsUnited States
LAST PAGES