XtGem Forum catalog

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah *KADDARA TA RIGA FATA 002*
ii. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya
Samu Sauki.
Ana haka ne sai kwatsam Annabi Sallallahu Alaihi
Wasallama ya samu sauki har ya umurci iyalinsa
su kai masa ruwa ya yi wanka. Samun wannan
kuzari da Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallama ya yi sai ya fita Masallaci har ma ya
samu sukunin yin huduba wadda a cikinta ya yi
addu’a ga wadanda su kayi shahada a yakin
Uhudu, ya tsawaita addu’a gare su.
Sannan ya ce ma mutane,“ku sani Allah ya bai
wa wani bawansa za6i a tsakanin rayuwar duniya
da koma ma Allah, amma wannan bawan ya zabi
abin da ke wurin Allah”. Mafi yawan Sahabbai ba
su gane in da maganar ta nufa ba sai da suka ga
Abubakar yana kuka, yana cewa, a’a Manzon
Allah! Mun fanshe ka da iyayenmu da
ubanninmu!!
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi
umurni a cikin hudubarsa da a tabbatar da ganin
rundunar da ya tura don ta yaki Rumawa a
karkashin jagorancin Usamatu Dan Zaidu ta tafi.
Ya bayyana ma jama’a cewa, ya ji maganganun
da ake yi game da kuruciyar Usamatu. Ya ce, to,
ai babansa ma haka ku ka ce masa.
Sannan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama
ya yi ma Muhajirai wasicci akan Ansaru, ya ce,
“Ya ku Muhajirai ku sani Ansaru su ne mafakar
Musulunci. Don haka ku kyautata ma wanda ya
kyautata a cikinsu, wanda ya munana a cikinsu
kuwa ku yafe masa”. Kamar dai yana nuni ga
cewa, Muhajirai za su rike al’amarin mulki a
bayansa, to kar su watsar da ‘yan uwansu, masu
masaukinsu, mutanen Madina.
Bayan haka sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallama ya fadi falalar Abubakar yana cewa,
“Ku sani ba ni da wani aboki kamar Abubakar,
kuma ba wanda Allah ya amfane ni da dukiyarsa
kamar Abubakar. Kuma da ya halalta in riki wani
badadayi a cikin mutane da shi zan za6a. To,
amma bai halalta ba domin Allah ya riga ya rike
ni badadayinsa kamar yadda ya riki Ibrahimu. Don
haka dai shi abokina ne a imani har Allah ya
hada mu da shi a aljanna”.
Sannan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama
ya ba da umurnin a rufe duk kofofin da mutane
suka bude wa kansu na zuwa Masallaci, ya ce,
amma a bar ta Abubakar.
*Abin Lura*
* Baban Usamatu, Zaidu Dan Harithah yana cikin
jagorori uku wadanda suka yi shahada a yaqin
Mu’utah.
* Watakila wannan shi ne nuni na karshe da
Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi ma
sahabbai game da jagorancin da yake son a
damka ma Abubakar na wannan al’umma, amma
ba ya son ya tilasta, ya fi son al’umma ta za6a
da kanta don ya zamo abin koyi har abada. A
nan
_Mu hadu a rubutu na gaba…………_
*Rubutawa:*
*_Dr. Mansur Ibrahim Sokoto_*
2018-06-19 09:48
* local_data-1529401735.36.dat · text/plain · 0B
· Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 5 user
This Week : 76 user
This Month : 63 user
Total all : 270329 visitors
LAST PAGES