XtGem Forum catalog

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah *KADDARA TA RIGA FATA 003*
iii. IDAN AJALI YA YI KIRA..
Kafin Usamatu ya bar birnin Madina sai da ya zo
ya yi bankwana da Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallama. Gurin Usamatu ne ya ga ya ji wasu
kalmomi daga wurin Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallama tun da yake ga halin da ake
ciki.
Amma ina! a wannan lokaci ciwo ya sake zagayo
shi har ma ba zai iya furta kalma guda daya ba
da bakinsa. Don haka sai Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallama ya rinka motsa yatsansa yana
nuna wa Usamatu cewa, yana yi masa addu’a da
zuci.
Daga karshe dai sai aka ji Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallama yana fadin “Na za6i
abokin sama.. Na za6i abokin sama.. Na za6i
aljanna…” Sannan rayuwarsa mai tsarki ta fita.
Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un.
Kafin wannan, Abubakar ya samu kwanaki da
dama bai ziyarci iyalinsa11 ba wadda ta ke a
Sunhu wani kauye mai nisan mil daya daga
Madina a dalilin kulawarsa da Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallama da kuma tsayar da
sha’anin ba da Sallah da aka dora masa.
Amma ganin sauki ya samu sai ya tafi can domin
ya ziyarci matarsa.
Isowarsa ke da wuya sai ya tarar duk wuri ya
rude, mutane suna ta kuka.
Umar kam har ya zare takobinsa yana barazanar
sare kan duk wanda ya kuskura ya ce Manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya mutu.
Abinka da sadauki sai Abubakar duk ya fita
batunsu, ya shiga dakin ‘yarsa A’ishah wurin da
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama yake
kwance, ya kware mayafi daga fuskarsa, ya
hakikance lallai Manzon Allah kam ya gama da
duniya. Nan take sai ya sunkuya ya sumbace shi,
ya ce, “na fanshe ka da uwata da ubana ya
Manzon Allah! Kai tsarkakakke ne a raye ko
bayan cikawa”.
Fitowarsa ke da wuya sai Abubakar ya hau
mimbari, daman dai Annabi Sallallahu Alaihi
Wasallama ya nada shi liman, kuma aikinsa bai
kare ba sai in Musulmi sun za6i wani sun ce shi
ya saurara.
Abin da ko Musulmi a wannan lokaci ba za su
ta6a yi ba ke nan.
*Abin Lura*
* Gaba za mu ga yadda Annabi Sallallahu Alaihi
Wasallama ya rinka yin ishara game da Abubakar,
har ma sai ya yi kamar ya fito fili sai ya fasa.
* Sunanta Habibatu Diyar Kharijah. Ita ce
amaryarsa da ya bari da cikin Ummu Kulsum.
_Mu hadu a rubutu na gaba…………_
*Rubutawa:*
*_Dr. Mansur Ibrahim Sokoto_*
2018-06-19 00:52
* local_data-1529401927.11.dat · text/plain · 0B
· Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 13 user
This Week : 69 user
This Month : 56 user
Total all : 270322 visitorsUnited States
LAST PAGES