Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah KADDARA TA RIGA FATA 004*
iv. KO WACE RAI MAI DANDANAR MUTUWA CE
A cikin hudubar da ya yi, Abubakar ya ba da
tabbaci game da mutuwar Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallama, kuma ya tsoratar da
duk mai tunanin cewa hakan ya kawo karshen
addini. Ya karanta wasu ayoyi na Alqur’ani don
kwantar da hankalin mutane.
Babu yadda za ka iya suranta kidimuwa da
tashin hankalin da ya samu Musulmi a kan jin
wannan labari sai fa in ka ji yadda A’ishah Uwar
Muminai ta siffanta su. Ga abin da ta ce:
Mutuwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallama ta sanya mutane suka koma kamar
bisashe da suka fada wani daji a cikin duhun
dare, ga hadari ya taso, ga namun daji a kewaye
da su.
Ita ko Nana Ummu Salmah cewa ta yi, wallahi ba
ta gaskata cewa, mutuwa ce Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi ba sai bayan
wuni biyu da ta ji ana gina da fartanya a dakin
A’ishah.
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya rasu
a ranar litinin 12/3/11 bayan hijira. Jama’a kuma
sun ci gaba da yi masa Sallah a tsawon wunin
litinin da talata Sannan aka kwantar da shi a
makwancinsa a dakin Nana Aishah da dare, gaf
da wayuwar garin Laraba.13 An yi jinkirin
jana’izar ne zuwa wannan lokaci saboda ba da
dama ga mutanen da su kayi tururuwa daga ko
ina zuwa wurin jana’izarsa, duk da haka kuwa
wasu sun tarar da an riga an gama.
*MADOGARA*
* Duba Muwadda’ Malik tare da sharhin Zarkani
(2/67) da kuma Littafin al Istidhkar na Imamu
Ibnu Abdil Barri (3/55).
* Duba Al Siratun Nabawiyyah na Ibnu Hisham
_Mu hadu a rubutu na gaba…………_
*Rubutawa:*
*_Dr. Mansur Ibrahim Sokoto_*
2018-06-26 23:33 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 9 user
This Week : 80 user
This Month : 67 user
Total all : 270333 visitors
LAST PAGES

XtGem Forum catalog