XtGem Forum catalog

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah *KADDARA TA RIGA FATA 005*
_Me Ya Faru Bayan Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallama?_
*Babi na Daya:*
*_Khalifancin Abubakar Dan Abu Kuhafah R.A_*
1. _Abubakar na Manzon Allah_
1.1 *Sunansa:*
Cikakken sunan Sahabi Abubakar shi ne,
Abdullahi Dan Usmanu Dan Amiru Dan Amru Dan
Ka’abu Dan Sa’adu Dan Taimu Dan Murratu.
Zumuncinsa da Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallama ya hadu ne a kakansa na shida
“Murratu” wanda shi ma kaka ne na shida ga
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama.
Ana yi masa lakabi da “Atiku”, ana kuma kiransa
Abubakar, sannan ya shahara da “Siddiku”, sunan
da ya samu bayan da ya gaskata Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallama a lokacin da mutane
ke karyata shi.
1.2 *Iyayensa:*
Sunan Babansa Usman. Ana kuma yi masa
alkunya da Abu Kuhafa. Mahaifiyarsa sunanta
Ummul Khair, Salmah Diyar Sakhr ita ma daga
kabila daya ta fito da babansa, wato kabilar Banu
Taim wadda karamar kabila ce kwarai idan aka
kwatanta ta da irin Banu Abdi Manaf da Banu
Makhzum da sauransu.
1.2.3 *Haifuwarsa:*
An haife shi a garin Makka a shekara ta hamsin
da daya kafin Hijira. Don haka Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallama ya girme shi da
shekara biyu da watanni kadan.
1.3 *Siffofinsa:*
Abubakar mutum ne fari, Siriri, Mai zurfin ido, da
babban goshi. Ga shi kuma ya dan sunkuya
kadan. Saboda sirirantakarsa, wando ba ya
dauruwa da kyau a qugunsa.
1.4 *Dabi’unsa da Halayensa:*
Abubakar Raliyallahu Anhu ya kasance daya daga
cikin fitattun ‘yan kasuwa masu fatauci. An
bayyana shi da halin kirki da kyauta. Kuraishawa
na darajanta shi saboda dattakunsa da
karimcinsa. Yana daga cikin abin da ke bayyana
kaifin hankalinsa, haramta wa kansa shan giya da
ya yi shi da abokinsa Usman Dan Affan. Ba
wanda ya ta6a kur6a ta daga cikinsu tun kafin
bayyanar Musulunci.
An ba da labarin cewa, tun asali Abubakar ya
haramta wa kansa shan giya ne saboda ya ga
wani mutum da ya bugu da ita yana sanya
hannunsa a cikin najasa ya kuma nufi bakinsa,
kana idan ya ji wari sai ya janye hannunsa daga
bakin. Daga nan ne Abubakar ya kyamace ta har
ya yi rantsuwa ba zai sha ta ba.
Haka ma bai ta6a bautar gumaka ba domin da
Allah ya nufi kawar da shi daga wannan sai
mahaifinsa ya je da shi yana yaro ya kai shi a
wurin gumaka ya sanar da shi cewa, ga
iyayengijinsa nan wadanda ake bauta, ya tafi ya
bar shi a nan. Shi kuma Abubakar da ya ji yunwa
sai ya roqe su abinci bai ji sun ce masa uffan ba,
ya roke su ruwa ba su ce masa ci kanka ba.
Daga nan ya tofa ma su yawu, ya zage su, ya
tafiyarsa yana mai tsananin kyamarsu da kaurace
masu.
Haka ma Abubakar bai iya waka ba. Ba za mu yi
mamakin wadannan dabi’un na Siddiqu ba sanin
cewa, shi babban aboki ne, masoyi ga
shugabanmu Sallallahu Alaihi Wasallama tun
zamanin kuruciya har manyanci. Mutum na kirki
kuwa daga abokanshi ake ganewa.
*ABIN LURA*
* Hikimar da ke cikin wannan ita ce, kasancewar
mawaka sun fi kowa yawan karya da kawata ta,
sai Allah ya kare Manzonsa da amintaccen
Manzon nasa daga aukawa cikin wannan hali.
_Mu hadu a rubutu na gaba…………_
*Rubutawa:*
*_Dr. Mansur Ibrahim Sokoto_*
2018-06-26 23:34 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 8 user
This Week : 79 user
This Month : 66 user
Total all : 270332 visitors
LAST PAGES