Pair of Vintage Old School Fru

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah *KADDARA TA RIGA FATA 006*
1.5 *Iyalinsa:*
Abubakar Raliyallahu Anhu ya auri mata biyu
kafin Musulunci, biyu bayan Musulunci. Matansa
na farko sun hada da:
1. Qutailah Diyar Abdul Uzzah, wadda ta haifa
masa Abdullahi da Asma’u.
2. Ummu Ruman Diyar Amir ‘yar kabilar Kinanata,
wadda ta haifa masa Abdul Rahman da Uwar
Muminai A’ishah.
Matansa na daga bisani kuwa sun hada da:
1. Asma’u Diyar Umais, wadda ta fara auren
Ja’afar Dan Abu Dalib. A bayan rasuwar Abubakar
kuma ta auri Ali Dan Abu Dalib. A ko wane gida
daga gidajen uku da ta yi aure ta haifi
Muhammad. A wurin Ali kuma ta haifi Yahya da
Aunu kamar yadda za mu gani a nan gaba.
2. Habibah Diyar Kharijah daga cikin Ansaru
(Mutanen Madina), ya rasu ya bar ta da cikin
‘yar autarsa Ummu Kulsum.
1.6 *Matsayinsa Kafin Zuwan Musulunci:*
Abubakar ya yi fice a zamanin jahiliyyah da ilmin
da ake kira Ansab, sanin dangantakar mutane da
tarihin gidajensu da abubuwan arziki ko rashin
arzikin da suka gudana a tsakanin mutane ko a
tsakanin kabilu. Sannan kuma shi ne wakilin
reshen gidansu a majalisar zartastawa ta
Kuraishawa wadda ta hada rassa goma na
wannan Kabilar, ko wane gida yana da aikinsa da
wanda yake wakilatarsa. Ga su kamar haka:
1. Banu Hashim: Su ke kula da shayar da
alhazzai ruwa. Wakilinsu a Majlisa shi ne Abbas
Dan Abdul Muddalib, baffan Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallama. Wannan ofis nasu ya
ci gaba da aiki bayan zuwan Musulunci.
2. Banu Umayyah: Su ke rike da tutar Kuraishawa,
kuma su ke rikon kwarya duk lokacin da aka rasa
shugaba kafin a hadu a kan sabon da za a nada.
Wakilinsu a Majlisa shi ne Abu Sufyan Dan Harb.
3. Banu Naufal: Su ke kula da asusun tallafi na
taimakon alhazan da guzuri ya yanke masu.
Wakilinsu shi ne Al Haris Dan Amir.
4. Banu Abdid Dar: Su ke kula da wanke Ka’aba
da tufatar da ita. Wakilinsu shi ne Usman Dan
Dalha.
5. Banu Asad: Su ke da ofishin Sakatariya. Duk
shawarar da aka yanke su ke sa mata hannu
kafin a aiwatar da ita. Wakilinsu shi ne Yazid Dan
Zam’ah Dan Aswad.
6. Banu Taim: Su ke da alhakin hada kudi don
biyan diyya idan aka sasanta masu fada da kuma
biyan bashi idan wani bakuraishe ya kasa.
Wakilinsu shi ne Abubakar Dan Abu Kuhafa.
7. Banu Makhzum: Su ke kula da wurin ajiyar
kayan yaki. Wakilinsu shi ne Khalid Dan Walid.
8. Banu Adiyyin: Su ne masu kula da huldar
kuraishawa da sauran kabilu, musamman a wajen
sha’anin yaki da zaman lafiya. Kuma su ke da
alhakin shelanta darajojin kabilarsu don ta yi
kwarjini a idon sauran mutane. Wakilinsu shi ne
Umar Dan Khattab.
9. Banu Jumah: Su ke kula da kuri’ar da ake yi
don neman sa’a in za a yi tafiya ko ciniki ko aure
ko makamancinsu. Wakilinsu shi ne Safwan Dan
Umayyah.
10.Banu Sahm: Su ke kula da tattalin arziki da
abinda ya shafi gumaka. Wakilinsu shi ne Al
Haris Dan Qais.
*MADOGARA*
* Duba Tarikhul Islami, na Mahmud Shakir, Bugun
Al Maktab Al Islami, Beirut, Lebanon
_Mu hadu a rubutu na gaba…………_
*Rubutawa:*
*_Dr. Mansur Ibrahim Sokoto_*
2018-06-26 23:38 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 7 user
This Week : 78 user
This Month : 65 user
Total all : 270331 visitors
LAST PAGES