XtGem Forum catalog

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah *KADDARA TA RIGA FATA 007*
1.7 *Musuluntarsa:*
Masana tarihi sun ruwaito cewa, tun kafin wahayi
ya fara sauka ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallama Abubakar ya yi wani mafarki wanda
ya labarta shi ga babban malamin nan masanin
addinin Nasara da ake ce ma Bahirah. Sai ya
tambaye shi daga ina ka fito? Ya ce masa daga
Makka. Ya ce, kai wane iri ne? Ya ce masa,
Bakuraishe. Ya ce, mene ne sana’arka? Ya ce,
Fatauci. Bahira ya ce, idan Allah ya gaskata
mafarkinka to, wani Manzo zai bayyana daga
cikin jama’arka, za ka taimaka masa a
rayuwarsa, kuma ka wakilce shi bayan
mutuwarsa. A wata tafiya kuma da ya yi zuwa
kasar Yaman ya samu bushara mai kama da
wannan daga wurin wani malami daga kabilar
Azd.
A lokacin da Allah madaukakin Sarki ya aiko
Manzonsa, Abubakar bai yi wata wata ba ya
gaskata shi yana mai cewa, bamu ta6a gwada
karya a kanka ba, kuma ka cancanci manzanci
saboda tsaron amanarka da sada zumuncinka da
kyakkyawar zamantakewarka da jama’a.
Daga nan kuma Abubakar ya ci gaba da zama na
hannun daman Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallama har in da mai raba masoya ta raba
su.
1.8 *Gudunmawarsa Ga Addini:*
Kasancewarsa mutum mai arziki, dattijo, kuma na
hannun daman Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallama ya ba shi damar taimaka ma addinin
Musulunci ta hanyoyi da dama; A Makka ya
kasance mai ba da kariya ga Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallama daga musgunawa da
cin zarafin da mushrikai su ke masa. Har ma Ali
Dan Abu Dalib yake cewa, bayan mutuwar Abu
Dalib babu wanda yake ce wa kafirai tinkanzil
idan suna musguna ma Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallama sai Abubakar.
Ga kuma dukiyarsa da ya yi amfani da ita wajen
ci gaban addini har ma Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallama da kansa yake cewa, “Dukiyar
kowa ba ta amfane ni ba kamar yadda dukiyar
Abubakar ta amfane ni”.
Abubakar ya taya Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallama wajen kiran mutane zuwa ga
Musulunci inda ya janyo musuluntar kusan
dukkan mukarrabansa da amintattunsa kamar su
Usmanu Dan Affan da Zubairu Dan Awwam da
Dalhatu Dan Ubaidullah da Abdur Rahman Dan
Aufu da Sa’adu Dan Abu Waqqas wadannan
dukkansu suna cikin mutane goma da Manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi wa
bushara da aljanna. Sannan daga bisani ya
musuluntar da Usmanu Dan Maz’un da Amiru
(Abu Ubaidah) Dan Jarrah da Arkamu Dan Abul
Arkam da Abu Salamata al Makhzumi wadanda
su ne magabatan farko a shiga Musulunci.
Abubakar ya gina wani karamin Masallaci a
farfajiyar gidansa da ke Makka inda yake Sallah
da karatun Alqur’ani. Ga shi kuwa mutum mai
dajin sauti da laushin murya wadda yake garwaya
ta da kukan tsoron Allah, abinda ya sa da dama
daga talakawan Makka suka rinka zuwa
saurarensa, wasunsu kuma a dalilin haka suka
musulunta. Kuma duk barazanar da mushrikai su
kayi masa a kan wannan ba ta sa ya daina ba.
A lokacin da yawan musulmi ya kai mutum
tamanin da uku sai Abubakar ya nemi Manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da su fito fili su
yi kira zuwa ga gaskiya. Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallama ya lurar da shi irin hadarin da
ke tattare da daukar wannan mataki a daidai
wannan lokaci, amma Abubakar ya nace akan
cewa sai su gwada sa’arsu. Hakan ko aka yi. To,
amma fa ba wanda ya biya harajin wannan
kasada sai shi Abubakar din. Domin kuwa fitowar
su ke da wuya, da suka isa masallaci sai
Abubakar ya tashi don ya gabatar da Manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallama zuwa ga
mutane. Ai kuwa ba su bari ya rufe bakinsa ba
sai suka fara yi wa musulmi a ture cikin
masallaci mai alfarma. Nan take kuwa suka
tarwatsa taron musulmi. Sannan suka far ma
Abubakar da duka har sai da suka kai shi kasa.
Sannan Utbatu Dan Rabi’ata ya dale akan cikinsa
yana amfani da takalma wajen dukan fuskarsa.
Bai gushe ba yana yi masa duka har sai da
hankalinsa ya gushe, fuskarsa ta yi jina jina har
ba a iya banbanta hancinsa da bakinsa.
Kabilar Abubakar ta Banu Taimin sun yo ciri don
su ceci dan uwansu. Amma ko da suka zo gayya
ta gama aiki, mushrikai sun yi ta’adin da suke so
akan Abubakar. Suka dauke shi a halin suma
suna tsammanin ya mutu suka kuma lashi
takobin idan ya mutu zasu kashe Utbatu Dan
Rabi’ata abinda kuwa da ya faru babu shakka zai
haifar da wani gagarumin yaki a tsakanin
kuraishawa. Amma sai Allah ya kiyaye, Abubakar
ya farfado can a cikin dare. Kalma ta farko kuwa
da ta fito bakinsa ita ce, ina Manzon Allah?
_Mu hadu a rubutu na gaba…………_
*Rubutawa:*
*_Dr. Mansur Ibrahim Sokoto_*
2018-06-26 23:42 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 1 user
This Week : 72 user
This Month : 59 user
Total all : 270325 visitors
LAST PAGES