XtGem Forum catalog

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah *KADDARA TA RIGA FATA 008*
1.9 *Damana mai ban samu:*
Abubakar ya yi amfani da dukiyarsa wajen sayen
bayi, talakawa wadanda ake azabtar da su a kan
Musulunci kamar Amiru Dan Fuhairata wanda
yake ya hada uwa da ‘yarsa Nana A’ishah.
Abubakar ya saye shi daga hannun Zufail Dan
Abdullahi Dan Haris wanda yake azabtar da shi,
Sannan Abubakar ya ziyauta shi, ya samu damar
yin addininsa har ma ya halarci yake – yaken
Badar da Uhud, ya kuma samu shahada a yaqin
Mu’unah.
Haka shi ma Bilal Dan Abu Rabah (Ladanin
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama
Abubakar ya same shi ana azabtar da shi sai ya
saye shi daga mai gidansa Umayyatu Dan Khalaf,
ya ziyauta shi. Shi ma kuma ya halarci yake –
yaken
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Sai
Zinnirah, wata baiwar Allah da Umar Dan
Khaddabi ya mallake ta kafin musuluntarsa, ya
kuwa rinka azabtar da ita har sai da ta rasa
idanunta, Sannan sai Mushrikai suka ce, Lata da
Uzza sun la’ance ta shi ya sa ta ma kance.
Amma imaninta da Allah ya sa Madaukakin Sarki
ya mai da mata da ganinta, sai suka ce, wannan
yana cikin sihirin Manzon Allah. A kan wannan
baiwar Allah da izgilin da mushrikai ke yi wa
Musulunci a kanta aya ta sha daya daga suratul
Ahqaf ta sauka. Abubakar ya fitar da ita daga
kangin bauta don ta samu ‘yancin ba da tata
gudunmawa ga addinin Allah.
Ba wadannan kadai Abubakar ya saya ya ‘yanta
su saboda Allah ba, akwai wasu bayi daga
kabilun Banu Adiyyin da Banu Abdi Shamsin su
ma sun more ma karimcin Abubakar da kishinsa
ga addini wajen samun wannan babbar gara6asar
da yake neman yardar Allah da Manzonsa a
kanta.
1.10 *Wasu Daga Cikin Darajojinsa*
Babu wani daga cikin Sahabban Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallama wanda ya tara
darajoji, musamman wadanda ya ke6anta da su
kamar Abubakar.
Daga cikin darajojinsa akwai tsananin kusancinsa
ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da
kasancewarsa abokin sirrinsa. Misali shi kadai ne
wanda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama
ya sanar da shi yana son Hafsah kafin ya yi
maganar aurenta.
Ga kuma ayoyin Alqur’ani da suka sauka suna
yaba ma halayensa na jarunta da karimci da
tsoron Allah.
Ga shi kuma ya tara dukkan ayyukan alheri da
suka sa za a kira shi ta dukkan kofofin aljanna.
Ga kuma fifikonsa na ilmi a kan sauran Sahabbai,
domin dukkansu sun aminta cewa, bayan dai ya
ke6anta da sanin ilmin nasaba (Dangatakar
mutane da sanin tarihin kakanninsu) kuma shi ne
ya fi su ilmi daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallama. Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallama ya yi mafarkin an kawo masa madara
a cikin wata kwarya sai ya sha har ta gudana a
tsakanin fatarsa da tsokarsa, Sannan sai ya bai
wa Abubakar. Sahabbai suka fassara wannan da
cewa, ilmin da Allah ya ba shi ne ya rage wa
Abubakar.
Sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya
ce, kun yi daidai! Kun yi daidai!!. Abubakar kuma
shi ne mafi tsentseni da tsoron Allah a cikinsu.
Saboda tsentseninsa ne ya ta6a amaye madarar
da ya sha domin ya yi shakkar halalcinta. Haka
kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama
ya ba shi shedar tawali’u da rashin girman kai a
lokacin da ya ce masa, kai ba ka jan wandonka
saboda girman kai.
Imaninsa kuwa ya rinjayi na sauran jama’a kamar
yadda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama
ya bayyana a wurare da dama.
Shi kadai ne yake fatawa a gaban Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallama, shi kuma kadai ne
yake wakiltarsa a abinda ya ke6ance shi kamar
limancin Sallah da jagorancin Hajji da
makamantansu.
*MADOGARA*
* Alal Misali duba Suratut Taubah aya ta 40 da
Suratuz Zumar aya ta 33 zuwa 35 da kuma
Suratul Lai aya 17 zuwa 21
* Duba Sahihul Bukhari da Sahihu Muslim
* Duba Sharhin Imam Nawawi a kan Sahihu
Muslim (15/150).
* Har a lokacin da Sahabi Abubakar ya zamo
khalifa bai daina tatsar madarar bisashe ba ana
biyansa, sai daga baya da al’amurran shugabanci
suka fi karfinsa. Wannan ma wani babban dalili
ne na tawali’unsa da rashin girman kai.
* Minhajus Sunnah, na Ibnu Taimiyyah,
_Mu hadu a rubutu na gaba…………_
*Rubutawa:*
*_Dr. Mansur Ibrahim Sokoto_*
2018-06-28 14:52 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 15 user
This Week : 71 user
This Month : 58 user
Total all : 270324 visitors
LAST PAGES