Teya Salat

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah Kar Ku taba daukar cewa masu wa'azi na sunnah KO mlamai na sunnah akwai wani Wanda nake adawa dashi ko nake fada dashi.
Dukkan Malamai na sunnah ina daukar su a matsayin yan uwanane,illa iyaka abuinda nakeson mutane su fahimta shine,
Cewar cewa muna da yan uwantaka bashi ke nuna baza muyi sabaniba,cewa munyi sabani bashi kenuna muyi fada KO muyi adawa da junaba.Abubakar da umar da usman da Ali duk sunyi sabani kuma wannan baisa sunyi fadaba.
kowa yayi Kira zuwa ga sunnah.
Babbar manufa dai ya kasance kanayi Dan Allah,kanaso ka raya sunnar manzon Allah.
قل كل يعمل على شاكلته فربكم أعلم بمن هو أهدى سبيلا.
Fatana ubangiji ta'ala ya jikanmu gaba daya,yayi mana gafara,ya fitar da hasaada da ganin kyashin juna,da rena juna daga cikin zukatanmu,ban fitar da kainaba daga wannan chutukaba,mu duka chutuka ne dake damunmu,ubangiji ta'alah ya bamu ikon tsira daga wannan chutuka na hassada da girman kai da rena juna da ganin kyashin juna.
Ubangiji subahanahu wata'alah yasa babbar manufarmu yaya za'ayi addini yaci gaba,yaya za'ayi barno dinnan ta maimata tarihinta na sheakara aru-aru data rike ta kafa daular musuluncida ta zamto haske ta zama garin qura'ani da ake zuwa daga ko ina ake koyansa.ya za'ayi ta zama garin qura'ani garin sunnar Manzon Allah (S.A.W).
Wannan shine babban fatanmu,wannan kuwa babu yadda za'ayi mu iya cin nasara sai mun yaki hassada da juna mun yaki kabilanci,mun yaki dukkan abinda zai kawo wargajewar Al'umma.mun dauka cewa addini shi kadai muka Sa aganmu Idan mukayi haka Allah zai sanya albarka cikin da'awarmu.
Wallahi tallahi idan bamuyi wannan ba ubangiji ta'alah sai ya turemu gefe guda sai ya kawo wasu kuma sai suyi.
Aida agaban idonku bamu bane mukeyi wasu ne sukeyi,an dauka cewa ma baza a iya saba musuba,ba Wanda ya isa yayi magana sai Wanda suka sawa albarka koya cire hula suka dafa kansa.
Sai wannan yazo ya wuce da basuyi da'awaba sai Allah ya kawo matasa zarata.
To haka idan na yanzun suke ganin sunkai wani matsayi muke gain munkai wani matsayi,muka kaucewa tsarin da muka taho akai muka shiga son rai da biyan bukatun juna.
فسوف يأتى الله بقوم يحبهم و يحبونه أذلة على المؤمنين أعزة على الكافرين يجهدون في سبيل الله ولا يخا فون لومةلاءم ذلك فضل الله يؤتيه من يشاء والله وسع عليم.
"Inayi mana fatan Alkhairi gaba daya Ina fatan kuyi mini afuwa,duk Wanda nayiwa ba daidaiba ya yafemin.duk Wanda nayiwa ba daidai ba Dan Allah ya yafe mini,KO mace KO namiji KO Wanda na sani KO Wanda bansaniba ko Wanda yake zuwa karatu KO Wanda baya zuwa,KO malami KO sauran mutane,duk Wanda nayiwa ba daidaiba Ina fatan ya yafe mini.
Ni duk Wanda yayi mini ba daidaiba KO wanene na yafe masa.da mace da namiji da tsoho da yaro da Wanda na sani da Wanda ban saniba, Dana kusa dana nesa.
Ina fata zamuyi juna adduoi na fatan alkhairi gaba daya.
2018-07-03 14:58 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 26 user
This Week : 49 user
This Month : 36 user
Total all : 270302 visitors
LAST PAGES