XtGem Forum catalog

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah MALAM INA SO NA HADU DA MIJINA NA FARKO A ALJANNA, KO ZAI YIWU ??
*_Tambaya_*
Assalamu alaikum Malam matar da mijinta ya mutu, sai ta yi wani auren, shin za ta sake haduwa da na farkon a lahira, in dukkansu sun shiga aljanna, ko kuma na karshen shi ne zai zama mijinta a can ? Amsa: To yar'uwa malamai sun yi sabani akan wannan mas'alar zuwa zantuttuka guda uku : 1. Za ta zauna da wanda ya fi kyawawan dabi'u a duniya. 2. Za'a ba ta zabi. 3. Za ta zauna da na karshensu. Wannan maganar ta karshe ita ce mafi inganci saboda fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi cewa : "Duk matar da mijinta ya mutu, ta yi aure a bayansa, to ranar lahira za ta kasance ga na karshensu" Albani ya inganta shi a Sahihu-jamiussagir a hadisi mai lamba ta : 2704. Wannan kuma shi ne dalilin da ya hana matar Abuddarda'a aure bayan mijinta ya mutu, lokacin da Mu'awiya ya nemi ya aure ta, ta ki yarda ta aure shi, saboda tana so ta zauna da abudarda'a a lahira . duba silsilasahiha hadisi mai lamba ta : 1281 Munawy yana cewa : "Malamai suna cewa : Wannan shi ne daya daga cikin dalilan da suka sa matayan Annabi s.a.w. ba su yi aure ba bayansa, saboda Allah ya riga ya kaddara cewa : matayansa ne a aljanna" duba Faidhul-kadeer 31 Allah ne mafi sani. Dr Jameel Zarewa
2018-02-08 00:23 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 6 user
This Week : 562 user
This Month : 804 user
Total all : 271070 visitorsUnited States
LAST PAGES