Polaroid

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah MASALLATAI DA YAWA NE SUKE SALLAR ISHA'I KAFIN LOKACINTA YA SHIGO:
1. Abin bakin ciki ne matuka irin yadda Masallatai da yawa suke kiran sallar Isha'i, suke kuma sallar Isha'in tun kafin lokacinta ya shigo a wannan yanki namu na arewacin Nigeria. Lalle wannan musiba ce cikin Al'ummah.
2. Misali: a nan garin Jalingo abin da yake rubuce a gurin mafi yawan masu ilmin falaki shi ne: daga yau din nan har zuwa 15 ga Ramadan lokacin sallar Isha'i zai shigo ne kama daga karfe bakwai da minti arba'in na dare, zuwa karfe bakwai da minti arba'in da uku na dare, watau (07:40pm - 07:43pm, to amma abin takaici za ku rika jin Masallatai da yawa a nan cikin garin Jalingo suna ta kiran sallar Isha'i tun daga karfe bakwai na dare (07:00), su kuma yi sallar da zarar sun gama yin kiran, saboda wai su masu son a yi wuf ne a gama da sauri domin a huta!!
3. Lalle abu ne mai kyau a san cewa haramun ne a kira salla kafin lokacinta ya shigo matukar dai ba sallar asuba ba ce.
4. Yana kuma da kyau a san cewa duk sallar farillar da aka yi ta kafin lokacinta na shari'ah ya shigo to lalle wannan sallar ba ta yi ba dole ne a sake yin ta.
5. Sannan dole ne al'ummarmu su daina wannan muguwar al'ada da suke yi a duk lokacin da watan Ramadan ya shigo, ta inda za a riga ganin Masallatai da yawa suna ta kiran sallar Isha'i kafin lokaci, suna kuma sallar Isha'in kafin lokaci, da hujjar yin sauri domin a gama a huta, lalle wannan aika-aika nau'i ne na yi wa Addini rikon sakainar kashi!
Allah muke roko da Ya sanya al'ummarmu a kan sunnar Annabisa mai tsira da amincin Allah har kullum. Ameen.
Dr Ibrahim Jalo Jalingo.
2018-05-21 09:14 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 19 user
This Week : 42 user
This Month : 65 user
Total all : 270248 visitorsUnited States
LAST PAGES