pacman, rainbows, and roller s

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah *_MATAR DA BA TA DA AURE, ZA TA IYA SANYA TURARE TA FITA UNGUWA?_*



*Tambaya*
 Assalam malam muna san karin bayani akansa turare gamata sufita, wani malami yace wadda ba matar aure ba zata iya sawa?


*Amsa*
Wa'alaikum assalam, To 'yar'uwa ya HARAMTA ga mace Baliga ta sanya turare, ta fita unguwaa, saboda fadin Annabi S.A.W: "Duk matar da ta sanya turare, ta wuce ta wani majalisi, to ta zama mazinaciya, kamar yadda Abu-dawud ya rawaito, A wani hadisin kuma yana cewa: "Duk matar da ta sanya turare, kar ta halarci sallar Isha tare da mu.

Nassoshin da suka gabata suna haramta sanya turare ga mace balagaggiya idan za ta fita, kuma ba su bambance tsakanin matar aure ba da budurwa ko bazawara, wannan sai ya nuna gamewarsu ga dukkan mata wadanda sharia ta hau kansu, tun da ba'a samu abin da ya kebance wasu nau'i ba, sannan kuma an haramta sanya turaren ne: saboda yana kaiwa zuwa tada sha'awar Maza, wannan kuma baya bambanta tsakanin matar aure da wacce ba ta yi ba.

Amma za ta iya sanyawa ta zauna a gida mijinta ya ji kamshi,  in ta yi hakan za ta samu lada. haka ma budurwa, za ta iya sanyawa a tsakanin 'yan'uwanta mata, ko gaban muharramanta wadanda ta san ba za su yi sha'awarta ba.


Allah ne mafi sani

22/6/1437
01/4/2016

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
2018-07-06 08:13 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 8 user
This Week : 31 user
This Month : 54 user
Total all : 270237 visitors
LAST PAGES