XtGem Forum catalog

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah ME YASA MAZA KE GUDUN AUREN
MA’AIKATA MATA?

Bisa bibiya da jin ra’ayoyin mutane,dalilai da
yawa sukan kawo wannan matsalar,wanda kashi
casa’in na matsalolin nan fa haka suke.
Masu magana sunce gaskiya daci gareta,amma
koda a kan kane yana da kyau ka fade ta.
Sannan zan so kada karanta wannan yasa kuyi
saurin yanke hukunci,ko ku zargi wani abu na cin
fuska a ciki,wannan farkon wasan ne,idan muka
yi hakuri zamu kai karshen matsalolin mu kuma
gano hanyar warware su
Ban qudurci yin wannan rubutu dan komai ba
face dan hasko wasu matsaloli da nemo
hanyoyin gyara a cikin su.
1.Mazaje da yawa na tsoron auren dukkan macen
da ke aiki,ballantana ace aikin ta ya shafi na
asibiti,saboda a cewar da yawan masu wannan
tunanin irin wadannan mata basu da kamun
kai,idan matan aure ne suna cin amanar
aure,zawarawa kuma dama ce ta same su na
barje gumi, yan matan ciki ake musu kallon
kananan zawarawan da suka san komai,sun san
yadda za su dauka su kuma zubda, sannan su
gyara jikin su tsaf kamar basu ba(Zargi).
Wannan ba karamin illa take yi ma ma’aikata
mata ba wajen samun mazajen aure,ko ci gaban
zaman lafiyar gidajen mazajen su.
Tabbas akwai masu shedana iya son ransu,da
aikata ayyukan kazanta ,musamman manyan
asibitoci ko ma’aikatu,hakan yasa ban taba jin
zafin namijin da ya kawo wannan dalilin matsayin
abinda zai hanashi auren ma’aikaciya ba,saboda
wlh wani abun ko nice naga matata a haka to fa
za a san abun yi.
Amma muyi ma kai adalci,duk lalacewa ba’a rasa
nono a ruga,akwai na Allah,a wani wajen aikin
ma sun rinjayi shaidanun a wani wajen kuma
shaidanu sun rinjaye su.
Shi yasa wasu malaman suke ganin koda aikin
asibiti ne to lallai ya kasance asibitin mata ne
zallah.
2.Gararin da tarbiyyar yaransu zata shiga:Wasu
mazan kuma basu da wancan tunanin,amma suna
kallon makomar tarbiyyar yaransu,a ya yin da su
suna waje iyalinsu da suka aura dan kula da
tarbiyyar yara suma suna waje,wanda wannan
matsayi ya samar da girmamawa ta musamman
2018-03-22 11:25 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 11 user
This Week : 31 user
This Month : 119 user
Total all : 270385 visitors
LAST PAGES