Polly po-cket

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah *MIJINA BA YA SON HAIHUWA, KO YANA HALATTA NA HANA SHI KAINA ???*
*Tambaya*
Assalamu alaikum. Malam ina da matsala tsakanina da mijina, baya son haihuwa ko saduwa muka yi saidai ya zubar a waje, Ga shi kuma yarinyar mu daya, ita ma bai damu da ita ba, ina da laifi In na hana shi kaina ??
*Amsa*
Wa alaikum assalam To 'yar'uwa yana da kyau ki Sani cewa ya Halatta a samu tazara a tsakanin iyali, abin da musulunci ya hana shi ne kin haihuwa kwata-kwata, saboda babbar manufar aure shi ne hayayyafa, don a samu wadanda za su bautawa Allah.
Zubar da maniyyi a wajan Farji ya halatta saboda hadisin Jabir wanda yake cewa "Mun kasance muna yin azalo (zubar da maniyyi a waje yayin saduwa) a lokacin da Qur'ani yake sauka, kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 4911.
Hadisin da ya gabata yana nuna cewa: Bai halatta mace ta hana mijinta kanta ba saboda hujjar yana AZALO, tun da Alqur'ani bai haramta ba.
Saduwa rukuni ne babba a aure, Wannan yasa Annabi S.A.W. ya ce: (Mace ta amsa kiran mijinta ko da tana kan kaskon tuya ya kira ta, sannan la'ana ta tabbata ga wacce mijinta ya yi fushi da ita, saboda ya neme ta ba ta ba shi hadin-kai ba.
Kula da abin da mutum ya haifa wajibi ne, ciyar da su kuma sadaka ne, Wannan yasa za ki dinga yiwa mijinki nasiha cikin ladabi don ya fahimci gaskiya .
Allah ne mafi sa ni
*Amsawa*
*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
2018-01-22 13:40 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 261 user
This Week : 555 user
This Month : 797 user
Total all : 271063 visitors
LAST PAGES