Insane

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah MUTANEN DA SUKE SUKAR SUNNAR ANNABI SUNA WASA NE DA ADDININSU:
1. Lalle masu sukar yin aiki da ingantattun hadithan Manzon Allah mai tsira da amincin Allah cikin wata mas'ala daga cikin mas'aloli da hujjar cewa su hadithan suna saba wa junansu, tabbas wadannan mutane suna wasa ne da addininsu, suna masa rikon sakainar kashi ne, kuma lalle hakan ba ya cutar da kowa sai kansu!
2. Idan har masu sukar yin aiki da ingantattun hadithai suka ce: Muna yin hakan ne saboda ana iya samun karo da juna a cikin hadithai a cikin mas'ala guda! to sai a tambaye su a ce: a cikin fatawowin shugabannin mazhabobi kuma karo nawa ne ake samu da junan a cikin mas'ala guda??
3. Tabbas babu wani kokari da masu guje wa yin aiki da ingantattun hadithai cikin wasu mas'aloli za su yi na nuna gazawa da kasawar hadithan manzon Allah mai tsira da amincin Allah face sai an sami dubun dubatan wannan abin da suke ganin kasawa ce a cikin fatawowin shugabannin mazhabobi ma.
4. Lalle haramun ne wani ya bar yin aiki da ingantaccen hadithi wanda yake nassi ne karara a cikin wata mas'ala daga cikin mas'aloli sannan ya koma ya rika yin aiki da fatawar wani shugaba daga cikin shuwagabannin mazhabobin da ake da su da hujjar cewa shi dan mazhaba kaza da kaza ne!
5. Dole ne al'ummar Musulmi a duk inda suke, a kuma ko wace mazhaba ne suke danganta kawuwansu zuwa gare ta su guje wa yin wasa da addininsu, su guje wa yin masa rikon sakainar kashi.
6. Lalle ne a cikin kabari babu mutumin da za a tambayi mamaci labarinsa in banda Annabi mai tsira da amincin Allah, lalle babu mamacin da za a tambaye shi labarin shugaban wata mazhaba daga cikin Mazhabobin nan da ake bi; domin babu wanda aka aiko daga cikinsu zuwa ga kowa.
7. Abu ne mai kyau a fahimci cewa: Shari'ah ba ta haramta wa kowa fa'idanta da maganar wata mazhaba daga cikin Mazhabobin nan da ake da su ba, to amma lalle ne Shari'ah ta haramta wa kowa gabatar da maganar wani a kan maganar manzon Allah mai tsira da amincin Allah. Allah Ka taimake mu. Ameen.
Dr Ibrahim Jalo Jalingo.
2018-05-09 23:27 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 8 user
This Week : 31 user
This Month : 18 user
Total all : 270284 visitors
LAST PAGES