XtGem Forum catalog

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah img

QALUBALENKU SHUGABANNIN MU NA WANNAN KASA! -Tijjani Hassan Gwale

Jiya ina sauraron Tafsirin Al-kur’ani me girma wanda Dr. Muhd Sani Umar R/lemo yake gudanarwa a garin bauchi gwallaga, malam yana tankade da rairaya acikin Suratul Marya, malam yazo dai-dai ayar nan da take cewa (YA YAHYA KUZIL KITABA BI QUWWA)
Malam yace ” shi koda yaushe addinin musulunci so ake ai masa roko na musamman me karfi, tamkar yanda alkur’ani yake fadawa Yahya, ba a so a rinka yiwa addini rukon sakainar kashi, ba a sassautawa a addini domin idan kana sassautawa to lokacinne za ai ta yi masa sako-sako.”
Malam ya kara da cewa” Wai anzo wajen mu ana neman fatawar mu akan cewa yara masu aikin SOJA suna son aikin soja sun samu sun tafi amma abin yaci karo da lokacin AZUMIN RAMADAN, wai suna jiran fatawa mu futo mu ce su sha azumi, ni bazan taba wata fatawa ba akan ace yara susha azumi domin suje aikin SOJA,
Wannan kalubale ne ga manya-manyan shuwagabannin mu a ce abu a shekara ana yinsa sau 29 ko 30 a shekara kuma wata guda a cikin wata goma sha biyu amma a rasa lokacin da za a rinka sawa sai lokacin da yaci karo da lokacin azumi, indai tsarin nigeriar za a bi kowa yana da ‘yancin sa, domin indai za a ce yaran su daina azumin sai sun gama to gobe ma za a nemi fatawa akan yaya za ai su daina Sallah gobe ma a ce su daina kaza su daina kaza,
Don haka ni bana goyon bayan wannan tsari kuma ya zama wajibi indai an yarda kowa yana da ‘yanci na shi na dan nigeria da kuma tabbatar da demokoradiyya:sorry: menene amfanin shugabannin mu da suke kusa da su dan su fada musu gaskiya su fada musu abin da addinin mu ya kunsa.”
Allah ya sakawa malam da Alkhairi da mafificin lada, ya sa shuwagabannin mu su duba wannan batu kuma sui aiki da wannan gaskiya, kuma sui mata kyakykyawar fahimta.
TIJJANI HASSAN GWALE
2018-02-05 13:21 (edited 2018-02-07 00:44 by ibnhujjah ) · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 2 user
This Week : 243 user
This Month : 485 user
Total all : 270751 visitorsUnited States
LAST PAGES